A yayin gudanar da aikinta na shugabancin karba-karba na BRICS, gwamnatin Brazil ta sanar a ranar 17 ga Janairun 2025, da amincewa da Najeriya a matsayin abokiyar hadin gwiwar kungiyar ta BRICS. Hakan na nufin Najeriya ta zama kasa ta tara na abokan huldar BRICS, tare da kasashen Belarus, Bolivia, Cuba, Kazakhstan, Malaysia, Thailand, Uganda, da Uzbekistan. Wannan sabon tsarin da aka kirkiro a taron kolin BRICS karo na 16 a Kazan a watan Oktoban 2024 na taka rawar gani wajen karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa da kuma sake fasalin tsarin mulkin duniya. A halin yanzu BRICS tana da cikakkun mambobi 10 da suka hada da Brazil, Rasha, Indiya, Sin, Afirka ta Kudu, Masar, Habasha, Indonesiya, Iran, Hadaddiyar Daular Larabawa yayin da wasu kasashe da dama suke kan hanyarsu ta shiga kungiyar. Kasancewar cikakken mamba na kungiyar na nufin samun damar inganta mu’amalar hada-hadar kudi da sauran kasashe mambobi da samun garkuwa daga mamayar kasashen yammacin duniya, tare da samun damar shiga tsarin manufofi da kudurorin kungiyar wadanda suka ginu a kan hadin gwiwar mutunta juna kuma a gudu tare don a tsira tare.
A matsayinta na abokiyar huldar kungiyar, Najeriya na iya amfani da damar wajen rage dogaro da tasirin dalar Amurka a harkokin da suka shafi hada-hadar kudi tsakaninta da sauran kasashe tare da karfafa yin kasuwanci da kudinta. Hakan kuma zai iya taimaka mata wajen magance matsalolin da ake fuskanta na saye da sayar da kayayyaki, wadanda ke ci gaba da zama manyan ginshikai a cikin matsalar tattalin arzikin kasar. Har ila yau, duk da cewa Najeriya ba cikakkiyar mamba ba ce, za ta iya samun damar samun kudade bisa wasu sharudda na musamman don gudanar da ayyukan samar da ababen more rayuwa da ayyukan raya kasa ta hanyar Sabon Bankin Raya Kasa (NBD) da Contingent Reserve Arrangement (CRA). A cewar wani rahoton Majalisar Kula da Huldar Kasashen Waje (CFR) da aka wallafa a watan Disamba, daya daga cikin manyan manufofin BRICS shi ne yin ayyukan da za su maye gurbin bukatuwar mambobinta zuwa ga Bankin Duniya da Asusun Lamuni na Duniya (IMF). Mambobin BRICS na fatan cewa wannan tsarin ba da lamuni na iya karfafa hadin gwiwar kasashe masu tasowa da kuma rage dogaro ga hanyoyin samar da kudade na gargajiya. (Mohammed Yahaya)