Hukumar NAPTIP ta kama mutane biyar da ake zargi da safarar mutane a Filin Jirgin Saman Nnamdi Azikiwe, da ke Abuja.
Hukumar ta kuma ceto mutane 24 da ake so yin safarar su.
- Da Haɗin Kai Da Jajircewa Ake Iya Tabbatar Da Dimokuraɗiyya – Shugaban AYCF
- NNPCL Ya Ƙulla Sabuwar Yarjejeniya Ta Samar Da Ɗanyen Mai Na Shekaru Biyu Da Matatar Dangote
Shugabar Hukumar NAPTIP, Binta Adamu Bello ce, ta jagoranci wannan samame na musamman a ranar Laraba.
Mai magana da yawun hukumar, Vincent Adekoye, ya bayyana cewa ɗaya daga cikin waɗanda aka kama tsohon jami’in tsaro ne, wanda ake zargin babban ɗan kungiyar masu safarar mutane ne da ke aiki a jihohin Kudu Maso Yamma.
Adekoye, ya ce wannan aikin na daga cikin sabon shirin da hukumar ta ƙaddamar domin yaƙi da safarar mutane, wanda ya shafi cibiyoyin ɗaukar ma’aikata da sauran wurare.
Bello, ta kuma bayar da umarnin ƙara tsaro a duk faɗin ƙasar na , musamman a tashoshin mota, hanyoyin ruwa a jihohin da ke bakin teku, da kuma filayen jiragen sama na ƙasa da ƙasa.
Samamen ya biyo bayan bayanan sirri daga masu ruwa da tsaki da abokan hulɗa, waɗanda suka sanar da hukumar cewa akwai mutane da ake shirin safararsu a filin jirgin Abuja.
Bayan kusan sa’o’i 6 da aka gudanar ana bincike, an kama mutane biyar da ake zargi, sannan an ceto mutane 24 da aka so yin safarar su.
Adekoye ya ce waɗanda aka ceto, masu shekaru tsakanin 15 zuwa 26 ne, kuma an ɗauko su daga jihohin Kano, Katsina, Oyo, Ondo da Ribas.
An shirya kai su Iraq, Sudan, Masar, Saudiyya, Bahrain da Afghanistan.
Wasu daga cikinsu ba su ma san inda ake son kai su ba.
Ɗaya daga cikin matasan ta ce an fada mata cewa za a kaita Turai domin ta yi aiki ta samu kuɗi a dalar Amurka, kuma iyayenta sun amince.
Wata kuma ta ce mahaifinta ne ya yaudare ta domin a yi tafiyar da ita,kuma ta rantse za ta kai shi ƙara.
Shugabar hukumar ta nuna musu bidiyon wasu ’yan Nijeriya da ke cikin mawuyacin hali a ƙasashen waje sakamakon irin wannan safara.
Ɗaya daga cikin matasan ta ce: “Na yi ƙoƙari na riƙe hawayena lokacin da na kalli bidiyon waɗanda ake azabtarwa. Idan haka ne ba zan je ba. Na fusata da mahaifina saboda ya yaudare ni.”
Bello ta yi Allah-wadai da masu safarar mutane da masu ɗaukar ma’aikata ba bisa ƙa’ida ba, waɗanda ke yaudarar ’yan Nijeriya domin su yi amfani da su ta hanyoyi daban-daban.
Ta ce ta gamsu da sakamakon aikin domin an samu nasarar karya hanyar wata babbar ƙungiyar masu safarar mutane da ke tura mutane zuwa ƙasashe masu hatsari, musamman a Gabas ta Tsakiya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp