A wani sumame na haɗin gwuiwa da gwamnatin jihar Kebbi da kuma jami’an hukumar NAPTIP tare da sauran jami’an tsaro suka yi, an yi nasarar ceto yara 19 da aka yi garkuwa da su a yankin Zuru a watan da ya gabata.
Gwamna jihar Kebbi Dakta Nasir Idris ya yabawa jami’an NAPTIP da ragowar jami’an tsaro kan matakin da suka ɗauka cikin gaggawa, yayin da ya kuma ba da umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa kan sace yaran da safarar su zuwa jihar Cross River.
- Kwamitin Tallafin Karatu Na Sanata Maidoki Ya Tantance Dalibai Sama Da 805 A Kebbi
- Dorinar Ruwa Ta Kashe Maigadin Lambun Sarki A Kebbi
Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a gidan gwamnati yau Litinin a Birnin Kebbi.
“Gwamnati za ta kula da yaran da aka ceto tare da ba su ilimi kyauta,” Ya kuma sha alwashin gurfanar da waɗanda suka aikata laifin a gaban Kuliya, yana mai cewa, “Dole ne mu tabbatar an gurfanar da waɗanda suka aikata laifin a gaban kotun da ta dace sannan kuma su fuskanci cikakken hukuncin shari’a.”
Gwamnan ya bukaci iyaye da masu kula da su da su sanya ido wajen kare ‘ya’yansu tare da ƙarfafa gwuiwar jama’a da su kai rahoto ga jami’an tsaro da suka dace yayin kula da abin da bai dace ba.