Fitaccen Mawakin da yake haskawa a yanzu, kuma mawakin da ya kware a fannin wakoki daban-daban na kowanne bangare kama Biki, Suna, Siyasa, Fim, Yabo, da dai sauransu, SALISU YARO DORAYI, ya bayyana cewa idan mawaka suka hada kansu to nasara ce abokiyar tafiyarsu in sha Allahu.
Ya kuma bayyana wa masu karatu ire-iren wakokin da ya yi ciki har da wadanda suke zaga wa ba tare da sanin mawakin da ya yi su ba, Mawakin ya bayyana dalilinsa na fara yin waka, har ma da wasu mahimman batutuwa da suka shafi rayuwarsa, ga dai tattaunawar tare da wakiliyarmu RABI’AT SIDI BALA Kamar haka;
Da farko za ka fada wa masu karatu cikakken sunanka da sunan da aka fi saninka da shi
Sunana Salisu Auwal wanda aka fi sani da Salisu Yaro.
Ko za ka fada wa masu karatu dan takaitaccen tarihinka?
To da farko dai an haife ni a ‘Karamar Hukumar Taura ta Jihar Jigawa’ na yi makarantar Firamare Dorayi Karama, na yi Sakandare a ‘Ulil Albab’ da ke unguwar Dorayi Kano.
Me ya ja hankalinka har ka tsunduma cikin harkar waka?
Da farko sha’awa abin yake bani kwarai da gaske.
Za ka yi kamar shekara nawa da fara waka?
Shekaru takwas da samun kaina a harkar waka.
Nawa ne adadin wakokin da ka yi?
Za su yi kamar guda 50.
Ko za ka fada wa masu karatu sunayen kadan daga cikin don su fahimta?
A duniya, Daukaka, Asin da Asin, Abokina, Kwalliya, Sayyadil Ambiya.
Wacce waka ce ka fara rubutawa kuma wacce ka fara rerawa a situdiyo?
Wakar yabon Ma’aiki na soma rubutawa wacce na soma rerawa kuma wakar soyayya ce.
Idan na fahimce ka kana wakar yabo kuma kana ta soyayya haka ne?
Tabbas! haka zancen ki yake, Har da ta biki da ta suna tare da ta siyasa.
Ko za ka iya fado wa masu karatu kadan daga cikin wadanda suka yi fice a kowanne bangare?
A bangaren wakar Soyayya akwai wakar fim din ‘A Duniya’, sannan akwai wakar Asin da Asin, Kwalliya da Mahaifiya da Abokina da kuma So Makahon Zuci. A bangaren Siyasa kuma akwai Makka saudia da Hakurin Rayuwa da kuma zaman duniya, Sai bangaren wakar Yabo akwai Sayyadil Ambiya, akwai Sayyadil Wara, Sai wakar biki akwai Azagaya akwai Zauna Amarya, akwai Shalelen Ango. Sai wakokin suna akwai sunan Muhammad akwai sunan ma’iz.
Kamar ita wakar A duniya kana nufin wadda ke tafiya cikin fim din ko kuma wata ce daban a ciki?
Eh! ita ce dai wacce take tafiya a cikin fim din A Duniya.
To a gaba daya wadannan wakokin da ka yi idan aka ce ka zabi guda ciki wacce za ka dauka?
Duka ina son su, to amma na zabi Mahaifiya. Abin da ya sa na zabe ta saboda na yi ta ne saboda mahaifiyata, labarin dake cikin wakar gaske ne, wannan ya sa ko wucewa na zo zan yi in na ji wani yana sauraren wakar ina jin dadi sosai sai na ji kamar na yi masa kyauta.
Cikin wakokinka wacce jama’a suka fi so?
Ita ce wakar A Duniya
Farkon da za ka fara waka shin ka nemi taimakon wani ne, ko da kanka ka zauna ka rubuta har ka buga?
A’a, na nemi taimakon wani, wanda ya taimaka min a lokacin kuma tare muka je da shi wurin shi ne Hamisu Breaker.
Ya ka ji lokacin da ka fara shiga situdiyo?
Tabbas na ji fargaba, amma saboda abokina Hamisu Breaker yana karfafa min gwiwa sai na ji kawai a raina zan iya, na fuskanci irin wannan matsalar saboda lokaci ne na farko a gare ni.
Me kake son cimma game da waka?
Ina da burin wakokina su shiga ko ina da ko ina a duniya, sannan su zama masu ma’ana da fadakarwa wannan shi ne burina.
Wanne irin kalubale ka fuskanta game da waka tun daga farkon farawarka kawo iyanzu?
Dankari! gaskiya suna da yawa, amma wanda na kasa mantawa da shi shi ne akwai wani lokaci aka je aka samu Iyayena aka ce musu harkar fim ba abu ne mai kyau ba, Iyayena suka sanya ido sosai sai suka gane ba haka bane harkar fim harka ce mai kyau da tsafta da kuma tura sako inda ba ka taba tunani ba, suka sanya min albarka tare da sahalewa na ci gaba da al’amurana.
To ya batun Nasarori?
Na samu nasarori masu tarin yawa wadanda ba za su lissafu ba, Alhamdulillah.
Wane abu ne ya taba faruwa da kai na farin ciki ko akasin haka da ba za ka iya mantawa da shi a rayuwa ba?.
Abin farin cikin da ba zan iya mantawa da shi ba lokacin da aka yi min kyautar mota.
Wane ne babban abokinka a cikin sauran mawaka?
Babban abokina shi ne Hamisu Breaker.
Da wa ka fi so ka yi waka?
Duk Mawaka Abokaina ne ina so na yi waka da su.
Ya ya ka dauki waka a wajenka?
Na dauki waka tamkar ni, ma’ana ba ni da sama da ita.
Bayan waka kana wata sana’ar ne?
Eh ina wata sana’ar, amma sirrina ne.
Ta ya kake iya hada sana’arka ta waka da kuma kasuwancinka?
Ai dukkansu lokaci ne da su, ina warewa kowanne a ciki na sa lokacin ba tare da na takura kaina ba.
To ya batun soyayya fa ko akwai wadda ta taba kwanta maka a rai da har ta kai da kun fara soyayya da ita cikin mawaka?
Gaskiya babu.
Idan wata ta ce tana sonka za ta aure ka cikin mawaka shin za ka amince ka aure ta ko ba ka da ra’ayin haka?
Kin san komai na Allah ne, ba zan iya yanke hukunci kai tsaye ba, amma dai abin da na sani zan kasance da duk wacce take kaunata.
Yaushe za ka yi aure?
Ba da jimawa ba In sha Allahu.
Wanne kira za ka yi ga masu kokarin fara waka?
Su yi hakuri kuma su nuna na ci a kan abin da suke so In sha Allahu watarana da sannu za su kai matakin da ba su taba zato ko tsammani ba.
Wanne kira za ka yi ga sauran mawaka ‘yan uwanka?
Mu ci gaba da hade kai mu zama tsintsiya madauri daya, nasara za ta zama abokiyar tafiyarmu, sannan mu ci gaba da tallafa wa mawaka masu tasowa domin watarana su ne madubin gobe.
Me za ka ce da masoyanka?
Salisu Yaro naku ne, ina kuma alfahari da ku, sannan ina jin sakonninku daga kan WhatsApp, Twitter, Facebook da Instagram da Tedt message, ku ne ni, Allah ya bar mu tare na gode.
Me za ka ce da makaranta wannan shafi na Rumbun Nishadi?
Hakika muna jin dadin yadda kuke bibiyar wannan kasaitaccen shafi na mu kuma muna yaba wa, muna tare da ku in sha Allahu mun gode.
Me za ka ce da ita kanta Jaridar LEADERSHIP HAUSA?
Ina rokon Allah ya kara daukaka ta ta ci gaba da haskawa a fadin duniya, muna Alfahari da wannan Jarida kwarai da gaske.
Ko kana da wadanda za ka gaisar?
Hamisu Breaker Dorayi, Abba Harara, Mudassir Isyaku, Abba Dorayi, Alhaji Ammar.
Muna Godiya Malam Salisu.
Ni ma na gode.