Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya taya Biodun Oyebanji murnar lashe zaben gwamnan Jihar Ekitii da aka gudanar a ranar Asabar.
Shugaban ya aike da sakon murnar ne cikin wata sanarwa da hadiminsa kan kafafen watsa labarai, Femi Adesina ya fitar, inda ya ce Oyebanji ya cancanci lashe zaben duba da irin gudunmawar da bayar wajen ci gaban Jihar.
- 2023: Masu Ruwa Da Tsaki A APC Sun Bukaci Zulum Ya Zama Abokin Takarar Tinubu
- PDP Ta Dakatar Da Dan Takararta Na Sanatan Kebbi Ta Tsakiya
Shugaba Buhari ya taya shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu da kwamitin yakin zaben jam’iyyar na kasa, kan nasarar da jam’iyyar ta samu na lashe zaben Jihar Ekiti.
“Wannan abun alheri ne a gare ka da kuma kwamitinka. APC na kara yin karfi kuma tana kara samun haduwar kai. Nasarar da aka samu a Ekiti ta nuna yadda ‘yan Nijeriya suka yi ammana da jam’iyyar wajen shugabanci na gari,” cewar shugaban kasa.
Ya bukaci mambobin APC da ke cikin gida da ketare da jajirce wanen ganin jam’iyyar ta yi nasara a babban zaben 2023 da kuma zaben gwamnan Jihar Osun da za a gudanar a watan Yuli.
Shugaba Buhari, ya taya al’ummar jihar Ekiti murna kan yadda suka gudanar da zabe cikin lumana da zaman lafiya wajen zabar shugaban da zai mulke su.
Ya jinjina irin aikin da hukumar zabe ta kasa (INEC), ta yi na gudanar da zaben yadda ya kamata.