Wasu bayanai na rahoto daga manhajar zuba hannun jari ta FXTM, ta yi hasashen cewa, sake zabar Donald Trump, a matsayin shugaban Amurka na 47, mai yuwa hauhawan farashin kaya munana a Nijeriya.
Kazalika, hakan zai iya aukuwa ne, saboda tashin farashin mai a fadin duniya, wanda hakan zai kuma iya shafar kudaden shiga da kasar ke samu a fannin na mai.
- Xi Jinping Ya Gabatar Da Jawabi A Taron Kolin CEO Na APEC
- Jimillar Darajar Kwangilolin Da Aka Daddale Yayin Baje Kolin CIIE Karo Na 7 Ta Zarce Dalar Amurka Biliyan 80
Taken rahoton shi ne, Nasarar Trump a Zaben Amurka! Menene manufarsa ga Nijeriya?
Wani babban fashin baki mai a kasuwanci Lukman Otunuga ne, ya fitar da rahoton.
Otunuga ya tabbatar da cewa, duba da yadda tsarin gwamnatin Trump zai iya shafar sauyin yanayin tattalin arzikin Nijeriya.
Ya kara da cewa, nasarar ta Trump, mai yuwa ta tilasta hauhawan farashin mai da iskar Gas, da ake amfani da su a cikin kasar wanda kuma hakan zai janyo kara samar da man na dogon zango.
Sai dai, tsare-tsaren nan a sa, ana ganin za su iya bunkasa tattalin arazikin Amurka.
Bugu da kari, hakan zai kuma kara yawan kudin ruwa na dogon zango, inda hakan mai yuwa ya sanya farashin mai ya ragu.
Hakan zai kasance abu mara kyau ga manyan kasashen da ke samar da man, musamman kasashen da suka dogara da samun kudaden shigar su daga man da suka sayar.
Kazalika, ga Nijeriya duba da kari da raguwar farashn mai a kasuwarduniya da kuma yadda dala ke kara samun daraja, hakan zai kara tabarbarar da hauhawan farashin kayan a Nijeriya.
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa, tashin dala da kuma na kwandalar Bitcoin sun tashi a ranar Larabar da ta wuce, bayan da ‘yan kasuwa suka yi hasashen samun nasarar Donald Trump. Kafin gudanar da zaben na Amurka.
Hakan ya sanya ake hasashen samun ragi a haraji da karin kudi da samun karin hauhawan farashin kaya.
A cewar rahoton dala ta tashi zuwa kashi 1.5, inda ta kai daidai da 154.33, ta takardar kudin yen, tun a watan Yuli.
Kazalika, ta tashi sama da kashi daya a kan takardar kudi ta EURO da kuma farashin ya karu zuwa kashi uku sabanin takardar kudi ta peso na kasar Medico.
A bisa jaddawalin S&P500, ya nuna cewa, ta karu zuwa kashi 1.4.
Wasu masu zuba hannun jari tuni sun yadda kasuwar ta kasance a lokacin da Trump ya shugabancin Amurka daga 2017 zuwa 2021.
Kazalika, yanayin kasuwar ya kai sama da kashi 60 a zangon mulkin Trump daga 2017 zuwa 2020, wanda tun daga wancan lokacin, ya ragu da kimanin kashi 10 a lokacin shugabancin shuga Joe Biden.
A cewarsa, sake dawowar Trump fadar shugaban kasa ta White House, zai iya haifar da karin yanayin na kasuwar a daukacin fadin duniya.
Kazalika, tunin karin kudin na Trump zai iya haifar da rige-rigen kasuwanci a nahiyar turai da kasar China wanda idan farashin ya karu zai sanya hauhawan farashi ga Amurkawa wanda hakan zai bunkasa dalar Amurka. Tuni dai, Trump ya lashi Takobin dakatar da yakin kasar Ukraine.