Rundunar ‘yansanda a Jihar Nasarawa ta tabbatar da aikata laifin yin garkuwa da mutane 75 a tsakanin watan Janairu zuwa Disamba 2023, kamar yadda alkaluman laifukan suka nuna. Bayanan da LEADERSHIP ta samu sun kuma yi nuna da cewa an kubutar da mutum 69 da aka yi garkuwa da su a tsawon lokacin da ake tsaka da bincike.
Hukumar ta tattara jimillar laifuka 839 a bara, da suka hada da garkuwa da mutane, fashi, fyade, kisa, da sauransu.
- ‘Yansanda Sun Kama Wasu Mutane 3 Da Ake Zargi Da Satar Jariri A Nasarawa
- Shekarau Ga Tinubu: Ka Rage Yawan Ministocinka Domin Rage Kashe Kudade
Alkaluman sun nuna cewa an tabbatar da rubuta laifuka 83 na fashi da makami; kisan kai, 38; fyade, 24; Sata, 202 yayin da aka sanya adadin sauran laifuffuka 417.
Wakilinmu ya lura da abubuwan da aka bayyana kamar, adadin satar da aka yi shi ne na fashi da makami wanda ya biyo bayan sauran laifukan a yawa, yayin da adadin fyade ya kai 24.
Alkaluman sun kuma nuna cewa, rundunar ta kwato makamai 49 da alburusai 607 a cikin wannan lokaci.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, DSP Ramhan Nansel, ya ce an samu bayanan ne saboda daukar matakan da ‘yansanda suka yi. Ya ce jami’an rundunar tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro na ‘yan uwa sun dukufa ba dare ba rana domin ganin an kawar da masu aikata laifuka a jihar, inda ya ce saboda irin wannan namijin kokari da aka yine aka tabbatar da wannan kididdiga ta laifuka.
Kuma an samu raguwar laifuka idan aka kwatanta da shekaru byu.
Ya ce kwamishinan ‘yansandan Jihar Nasarawa, Shehu Umar Nadada, ya ce rundunar za ta rubanya kokarin da take yi wajen yaki da masu aikata laifuka.