A zaman Majalisar Dattawa na ranar 20 ga Fabrairu, wata sabuwar taƙaddama ta kunno kai tsakanin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, da Sanata Natasha Akpoti Uduaghan mai wakiltar Kogi ta Tsakiya.
Sanata Natasha ta gabatar da ƙorafi kan Akpabio, inda ta zarge shi da cin zarafi da kuma tursasawa wajen hana ta gudanar da aikinta a matsayin ƴar majalisa.
Ta bayyana cewa Shugaban Majalisar ya yi amfani da matsayinsa wajen tauye haƙƙinta da ƙetare iyakarsa.
Yadda Rikicin Ya Faro
Rikicin ya samo asali ne lokacin da mai tsawatarwa na majalisar, Sanata Mohammed Munguno, ya bayyana cewa Sanata Natasha ta ƙi komawa sabuwar kujerar da aka ware mata.
Wannan ya haifar da gagarumin ce-ce-ku-ce har Shugaban Majalisar, Akpabio, ya umarci jami’an tsaro da su fitar da ita daga zauren majalisar.
Bayan haka, ƙungiyoyi da jama’a da dama sun buƙaci a yi bincike kan lamarin, wanda ya kai ga Majalisar Dattawa ta buƙaci Sanata Natasha ta bayyana kanta da kuma gabatar da ƙorafi a hukumance.
Sanata Natasha Ta Gabatar Da Ƙorafinta
A ranar Laraba ta gabatar da ƙorafin, Sanata Natasha ta isa majalisar ne tare da mai gidanta, sannan ta yi magana kai-tsaye ga Shugaban Majalisar.
Ta ce: “Ina gabatar da ƙorafi kan Shugaban Majalisar Dattawa, mai girma Sanata Godswill Akpabio, bisa cin zarafi, tursasawa da ƙoƙarin daƙile min aikina a matsayin ƴar majalisa.”
Daga nan, ta sauka daga kujerarta zuwa gaban Akpabio, inda ta rusuna tare da miƙa takardun ƙorafinta.
Martanin Akpabio
Sanata Akpabio ya karɓi ƙorafin Natasha, amma ya yi watsi da zarge-zargen da ta ke masa.
“Na miƙa wannan ƙorafi ga kwamitin ladabtarwa don yin nazari. Amma ina so na fayyace cewa ba ni da wata alaƙa da zargin cin zarafi da aka yi min.”
Ya ci gaba da cewa bai taɓa cin zarafin wata mace ba, yana mai bayyana cewa mahaifiyarsa ta koya masa mutunta mata.
Ya kuma ƙara da cewa yana da ‘ya’ya mata huɗu, don haka ba zai taɓa aikata abin da ake zarginsa da shi ba.
Ƴan Majalisa Ba Su Goyi Bayan Natasha Ba
Duk da cewa Sanata Natasha ta gabatar da ƙorafinta, kusan dukkanin ƴan majalisar da suka yi tsokaci ba su goyi bayan ta ba.
Hatta Sanatoci mata ƴan uwanta ba su mara mata baya.
Wasu sanatocin sun ce irin wannan ƙorafi bai dace a gabatar da shi a majalisa ba, yayin da wasu suka buƙaci a yi ganawar sirri kan batun.
Sai dai Akpabio ya ce hakan ba zai yiwu ba, domin akwai wakilai daga Birtaniya da suka halarci zaman majalisar domin nazarin yadda al’amura ke gudana.
Tuni lamarin ya janyo ce-ce-ku-ce a cikin majalisa da wajenta,
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp