Ƴansandan Najeriya sun karɓi wasiƙa daga Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, wadda aka dakatar daga wakiltar yankin Kogi ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, inda take neman a dawo da ita bisa hukuncin babbar Kotun Tarayya da ta soke dakatarwar da kuma bayar da umarnin dawowarta nan take.
A cikin wasiƙar da lauya Michael Jonathan ya rubuta a madadin Sanatar, wadda aka sanya ranar 16 ga Yuli, 2025, an mika ta ga Daraktan Shari’a da Shawarwari na Majalisar Tarayya, Charles Yoila. Wannan mataki ya biyo bayan wata wasiƙar da Majalisar ta aika ranar 14 ga Yuli, wadda ta bayyana hukuncin kotun a matsayin shawara kawai.
- Ba Zamu Dawo Da Sanata Natasha Zauren Majalisa Ba, Sai Mun Karɓi Kwafin Hukuncin Kotu– Majalisa
- Lauyoyin Natasha Sun Buƙaci Ta Koma Majalisa Ranar Talata Bayan Miƙa Takardun Hukuncin Kotu
Lauyoyin Akpoti-Uduaghan sun bayyana cewa kotu ta bayar da umarni guda goma sha biyu da kalmar “AN UMARTA DA HAKA” ke gaba, wanda ke nuna cewa umarnin yana da cikakken ƙarfi na doka. Suna kuma jaddada cewa hukuncin ya nuna dakatarwar da aka yi mata ya saɓawa sashi na 63 na Kundin tsarin mulki da kuma dokokin Majalisar Dattawa na 2023.
Matsalar musamman na cikin umarni na goma sha biyu inda kotun ta ce “Majalisar Dattawa ta dawo da wanda ake ƙara.” Yayinda Majalisar ke fassara “ta” a matsayin shawara, lauyoyin sun ce a cikin muhallin hukuncin da kuma cin zarafin doka da aka bayyana, wannan umarni ya zama tilas ne.
Sanatar Akpoti-Uduaghan ta sanar da Majalisar Dokoki niyyarta ta dawowa bakin aiki ranar 22 ga Yuli, 2025, bayan kammala lokacin makoki na tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari. Lauyoyinta sun gargaɗi Majalisar cewa duk wata tangarda da za a yi za ta fuskanci “dukkan matakan doka” domin tabbatar da bin umarnin kotu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp