… ci gaba
4) Amfani da shawarar wasu a kuma kara ingantasu: Manufa anan ita ce su shawarwarin na kowa ne, wannan kuma yana nufin su shawarwarin bana wanda ke da su bane, hakan shi yasa Malamin yana ba wadanda suka halarci koyon su ba saura kwarin gwiwa domin a kara ma wasu shawarwarin. Daganan kuma sai a gabatar da abinda ya wakilci ci gaba wajen hada wani abu,hakan kuma na nuna duk wanda yake koyo yana da dama ta yin kari ko kuma ragi.
Abubuwan da suke taimakawa wajen samun nasarar musayar ra’ayi kamar haka (Al-Mandalawi,2019):
1) Kyan aiki da dabaru da dokokin wajen hanyoyin musayar ra’ayi.
2) Abubuwan da aka koya da kuma maida hankali kan abinda ake yin a aikin Shugaba ko Malami, da kuma yadda yake Kallon lamarin gaba daya na lamarin da ya shafi musayar ra’ayi.
3) Ita koyarwar ana yenta a wani yanayi mai gamsarwa da nishadi, kar abin ya kasance mai bata rai.
4) Ana da matukar muhimmanci a shirya shi abinda za a koyar su kuma masu halartar kafin lokacin ya yi akan maudu’in da za a tattauna.
5) A amince da shawarwarin da ba a saba da su ba.
6) Duk hanyoyin da aka yi amfani da su ya dace a bi su dayin tambayoyi:Ta yaya za a bunkasa shawarar ? Hanyoyi nawa za a yi amfani da su wajen bunkasa shawarwari da kuma wasu lamauran?.
7) Yana da muhimmanci ga shi mutumin da zai jagoranci koyarwa ya gano ko dabarar da zai amfani da ita domin samun cimma burin saboda a gano yadda za a yi maganin yadda za a dinke barakar ta amfani da dabaru daban daban.
8) Ya kasance shine zai koyar da maudu’in daban daga cikin samun dabaru,bayyana su,sai gyarasu, duk da haka kuma ya kasance a shirye yake wajen habaka koyarwa wajen amfani da fasahar shi.
9) Koyarwar ta kasance tana da muhimmanci ta kasance ta yi nisa daga da shawarar da mutum yake Kallon ta yi ma shi, ya kuma zama an kare ta da danganta da abinda ko maudu’in da za a koyar.
10) A rubuta shawarwarin wadanda aka samu daga koyarwa domin ta haka ne dukkan wadanda ake koyamawa za su iya ganinsu.
11) A lura kwarai da gaske domin a cire masu lura da yadda ake koyar da maudu’in.Dukkan wadanda suke halartar koyarwar ya zama sun bada tasu gudunmawa saboda kasancewar mai lura da yadda ake koyarwar a wuri mai nisa lokacin da ake koyarwar,ba ma kamar idan ya kasance yana daga cikin muhimman mutane a babbar makarantar ko kuma makaranta a wurin da ake koyarwar,zai kasance a matsayin wanda zai bada kwarin gwiwa da kuma bada gudunmawa.
12) Mutumin da yake jagorancin koyar da maudu’in ya dace ya gane cewa shi lamarin karka juna ilimi bai kasancewa kashi 100 ya zama daidai wajen samun sabbin shawarwari. Bugu da kari kuma amfani da musayar ra’ayi ba kawai wata dama bace ta bada damar gabatar da sabbin shawarwari, har da akwai hanya ta wadanda ake koyamawa su gane wni abin kimiyyar da aka yi amfani da shi domin yin maganin lamarin da ke bada matsala a cikin koyarwar.
Luggogin da za ayi amfani dasu masu amfani wajen aiwatar da darasin musayar ra’ayi, daga cikinsu suna ganin yadda ake yin abin wato samun shawarwari suna tafiya ta hanyoyi ko kafofi uku (Al-Mandalawi, 2019):
1) Matakin a gano matsalar da kuma nazarinta wajen rarraba ta zuwa kananan abubuwan da ta kunsa, daganan kuma sai a tsara su yadda za’a gabatar ma wadanda za a koyamawa.
2) Matakin a gane yadda za ayi aikin,tare da sanini dokokin musayar ra’ayi.
3) Matakin a nazarin shawarwarin, zabarsu da kuma yin amfani da su.