Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Kasa (NCAA) ta dakatar da ayyukan jirgin sama na Max Air kirar Boeing 737 nan take.
Wannan na cikin sanarwar daraktan kula da ayyuka na hukumar, Kyaftin Ibrahim Dambazau da kuma babban daraktan hukumar, Kyaftin Musa Nuhu suka fitar.
- Kotu Ta Umarci DSS Ta Saki Emefiele Cikin Mako Daya
- Cire Tallafin Mai: Za A Kara Farashin Burodi A Nijeriya
A cikin wata wasika NCAA/DG/AIR/11/16/363, NCAA ta ba da umarnin dakatar da sufurin jirgin sama na Max Air Boeing 737 a cikin gida.
NCAA ta dakatar da sufurin kamfanin jirgin saman a cikin gida har sai lokacin da ta dage dakatarwar.
Hukumar ta ce ta dauki matakin ne saboda wasu al’amura da suka faru da jiragen Max Air kirar B737.
NCAA ta lissafa abubuwan da suka faru wadanda har suka sanya ta daukar wannan mataki.
A ciki har da lalacewar wasu sassan jirgin da ta janyo wani mummunan al’amari ga jirgin Boeing 737-400 tsakanin tashinsa daga filin jirgin sama a Adamawa zuwa saukarsa a filin jirgin Nnamdi Azikiwe da ke Abuja ranar 7 ga Mayu, 2023.
NCAA ta soke tashin jirgin Max kirar Boeing 737-400 mai lamba 5N-MBD a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano saboda fitar iskar gas a ranar 11 ga Yuli, 2023.
Hukumar ta kuma fara bincike game da harkokin kamfanin jirgin saman n Max Air.
Hukumar ta ce dole sai sun gamsu da sakamakon binciken, kafin ta bai wa jirgin Boeing 737-400 damar ci gaba da ayyukansa a Nijeriya.
A lokuta da dama ma’abota tafiye-tafiye a jirgin na Max Air sun sha kokawa kan yadda kamfanin ke saba alkawari wajen jigilar mutane zuwa wasu sassa na kasar nan.