Hukumar NCC ta amince da ƙarin kuɗin sadarwa na kamfanonin waya, bisa roƙon da suka gabatar. Mai magana da yawun hukumar, Reuben Mouka, ya ce an amince da ƙarin ne bisa tanadin dokar NCA ta 2003, wacce ta ba da ikon tsara kuɗaɗen sadarwa. Ya ce matakin ya zama dole sakamakon halin da tattalin arziƙi ke ciki.
Sabon ƙarin ya kai kashi 50% na kuɗin sadarwa na yanzu da ake biya, duk da wasu kamfanoni sun nemi ƙarin kashi 100%. NCC ta bayyana cewa, wannan gyara zai ba da damar ci gaba da zuba jari a fannin sadarwa, wanda zai taimaka wajen inganta ayyuka ga masu amfani da hanyoyin sadarwa.
- Gwamnatin Kaduna Ta Gargaɗi Jami’anta Kan Rubutu A Kafafen Sadarwa
- Yadda Fasahar Sadarwa Ta Bunkasa A Kasar Sin Zuwa Karshen 2024
Hukumar ta jaddada cewa ƙarin ba zai zama babban nauyi ga tattalin arziƙin masu amfani da hanyoyin sadarwa ba, don an tsara shi yadda zai kare masu amfani da kuma tabbatar da ɗorewar masana’antar sadarwa a Nijeriya. NCC ta umurci kamfanoni su bayyana sabon tsarin kuɗin ga jama’a tare da tabbatar da ingantattun ayyuka da sabbin fasahohin sadarwa.
Hukumar ta ce za ta ci gaba da aiki tare da masu ruwa da tsaki don gina masana’antar sadarwa mai ɗorewa da haɗin kai, wacce ke kare masu amfani, tallafawa kamfanoni, da kuma inganta tattalin arzikin fasahar sadarwa ta ƙasa baki ɗaya.