Hukumar da ke kula da gidajen gyaran hali ta Jihar Kano, ta yi tsokaci kan rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta, cewa fursunonin na fama da karancin abinci.
A cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Musbahu Lawan Kofar Nasarawa ya fitar, ya yi watsi da ikirari, inda ya ce karya ne, kuma an yi ne don a bata sunan hukumar.
- Mutum 2 Sun Rasu Yayin Da Bene Ya Rushe Da Su A Kano
- Nijeriya Ta Zama Kasa Ta 3 Da Ta Fi Karbar Bashin Bankin Duniya
“Wadannan rahotannin da ake yadawa abun takaici ne. Hukumarmu tana tabbatar wa jama’a cewa jin dadin fursunoni ne babban abin da muka sa gaba, duk da kalubalen tattalin arziki,” in shi.
Yanayin gidajen yari a Nijeriya ya dade da zama abin damuwa, tare da korafe-korafe dangane da rashin samun kula da inganta kiwon lafiya, samar da abinci da kuma takaita cunkoso.