Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) ta tarwatsa wasu manyan ƙungiyoyin dillalan ƙwayoyi masu safara tsakanin ƙasashe, inda ta kama wasu mutane shida da ake zargin jagororin kwayoyi ne daga Adamawa, Anambra, Legas, da Kamaru, tare da kwace hodar ibilis da sauran kwayoyi da darajarsu ta kai biliyoyin Naira.
Mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi, a yau Lahadi ya bayyana cewa a na sa ido kan waɗannan mutanen, da suka haɗa da Ibrahim Bawuro, Najib Ibrahim, Ibrahim Umar, Nelson Anayo, Ezeh Martin, da Adejumo Ishola, tsawon watanni.
- NDLEA Ta Bayar Da Shawarar Tilasta Wa Ma’aurata Yin Gwajin Shan Ƙwaya A Kano
- Wa Ke Da Gaskiya Tsakanin NDLEA Da Sanata Ashiru?
An ce ƙungiyoyin suna da hannu wajen samar da ƙwayoyi ga ƙungiyoyin ta’addanci da ke aiki a Nijeriya da Kamaru, inda jami’an NDLEA suka bibiye su ta hanyar garuruwan Mubi, Onitsha, da Legas.
A ranar 7 ga Oktoba, jami’an NDLEA suka cafke Bawuro da Najib a Taraba, bayan sun ɗauki wani kaya na ƙwayoyi a Onitsha. An kama su ne bayan sun tsere daga motarsu ɗauke da ƙwayoyi 276,500 na tramadol a kan babbar hanyar Jalingo-Yola, yayin da suke ƙoƙarin guje wa jami’an NDLEA.