Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) a Jihar Kano, ta samu nasara a shirinta na “Operation Hana Maye” na yaki da safarar miyagun kwayoyi a jihar.
Daga ranar 17 ga watan Janairu zuwa 26 ga watan Janairu, 2024 karkashin jagorancin Kwamandan jihar, Abubakar Idris-Ahmad, hukumar ta kama mutane 198 da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi tare da tarwatsa gidajen sarrafa miyagun kwayoyi 21.
Kakakin hukumar, Mista Sadiq Muhammad-Maigatari ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai.
Dakarun hukumar sun kai samamen ne wurare daban-daban, ciki har da wani gidan casu da ya koma wajen hada-hadar miyagun kwayoyi, inda aka kama mutane 61.
Har wa yau, an kama mutane 42 da ake zargi a makabartar Dan Agundi, sannan an tarwatsa gidajen miyagun kwayoyi guda 21 da ke makabartar Sheka da Sheka Obajana.
Daga cikin abubuwan da hukumar ta kwato har da maganin Exol, tabar wiwi, da sauran magunguna masu hatsari.
NDLEA ta sake jaddada aniyarta na kawar da shaye-shayen miyagun kwayoyi da safarar miyagun kwayoyi a jihar.
Hukumar ta ce za ta mayar da hankali wajen kara kaimi don zakulo masu safarar miyagun kwayoyi.
Kwamanda Abubakar Idris-Ahmad, ya bukaci jama’a da su sanya ido tare da kai rahoton masu safarar miyagun kwayoyi a jihar.