Hukumar NDLEA a Jihar Kano ta kama mutane 230 tare da kwace nau’ikan miyagun ƙwayoyi a wani sumame na tsawon kwanaki 30 da aka gudanar a wuraren da ake ta’ammoni da kayan maye. Kwamandan hukumar a jihar, Abubakar Idris, ya ce wannan mataki wani muhimmin ɓangare ne na ƙoƙarin dawo da zaman lafiya da rage laifuka a Kano.
Idris ya bayyana cewa sumamen ya gudana ne tare da haɗin gwuiwar rundunonin tsaro, ciki har da ƴansanda, NSCDC, hukumar shige da fice, hukumar gyaran hali, da DSS, waɗanda suka taimaka wajen kutsa kai cikin wuraren da ake boye miyagun ƙwayoyin. Ya ce wannan aiki ya biyo bayan bayanan sirri da aka tarar daga al’umma da hukumomi.
- NDLEA Ta Kama Malami Da Matarsa Da Buhunan Tabar Wiwi 360 A Kuros Riba
- NDLEA Ta Kama Kilo 588 Na Miyagun Ƙwayoyi, Ta Ƙona Hekta 6 Na Gonakin Wiwi A Adamawa
Rahoton ya nuna cewa manyan wuraren da aka kai sumame sun haɗa da Kofar Ruwa, da Tashar Rami, da Rijiyar Lemo, da Kurna, da Mil Tara, da Zage, da Dorayi Karshen Waya, da Dawanau. Sauran wuraren sun haɗa da Filin Idi, da Kasuwar Rimi, da Zango, da Kofar Mata, da Kano Line da Ladanai, inda aka gano cibiyoyin hada-hadar miyagun ƙwayoyi.
Daga cikin kayan da aka ƙwato akwai wiwi, da EXOL-5, da diazepam, da suck-and-die, da Sholisho, da codeine, da wasu makamai da masu safarar kayan maye ke amfani da su. NDLEA ta ce za ta ci gaba da irin waɗannan sumame, tare da ƙara matsa ƙaimi wajen daƙile shaye-shaye da fataucin miyagun ƙwayoyi a faɗin jihar.














