Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta cafke wani mai safarar miyagun kwayoyi, Chukwuemeka Clement, mai shekaru 67, a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, kan laifin safarar hodar iblis guda 100.
Wanda ake zargin ya ce ya shiga sana’ar safarar miyagun kwayoyin ne don ya samu isassun kudade don ya yi sabon aure ya watayawa.
- NDLEA Ta Kama Abubuwa Masu Fashewa 399, Da Haramtattun Kwayoyi A Neja
- NDLEA Ta Kama Tabar Wiwi Buhu 116 A Jihar Kano
Jami’in hulda da jama’a na hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, ya ce an kama Chukwuemeka ne a ranar Talata 3 ga watan Oktoba a lokacin da ake tantance fasinjojin jirgin Ethiopian Airline mai lamba 951.
A wani labarin makamancin wannan, a ranar 3 ga watan Oktoba kuma a Kano, jami’an NDLEA a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano (MAKIA), Kano, sun cafke wata mata mai suna Bilkisu Mohammed Bello, mai shekaru 45 a duniya, a lokacin da take shirin shiga jirgin saman Saudiyya don zuwa kasar ta Saudiyya.