• English
  • Business News
Sunday, October 19, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

NDLEA Ta Gudanar Da Bikin Ranar Yaki Da Sha Da Fataucin Miyagun Kwayoyi Na Duniya A Kebbi

by Sadiq
3 years ago
NDLEA

Hukumar Hana Sha da Fataucin miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), reshen Jihar Kebbi, ta bi sahun sauran jihohi da masu ruwa da tsaki wajen gudanar da bikin ranar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta duniya a jihar.

Bayan kudurin Majalisar Dinkin Duniya (MDD) a shekarar 1987, ranar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi na duniya da nufin karfafa aiki da hadin gwiwa don cimma burin al’ummar duniya da ba ta su ga muggan kwayoyi.

  • Mutane 3 Sun Mutu A Hatsarin Mota, Biyu Sun Jikkata A Kogi
  • G7 Ta Sha Alwashin Ci Gaba Da Taimakon Ukraine A Yakinta Da Rasha

Bikin na 2022 mai taken cewa” Magance kalubalen shan kwayoyi a cikin Lafiya da Rikicin Jin kai yana da matukar dacewa dangane da cutar ta Korona da karuwar kalubalen tsaro a Nijeriya”.

A shekarar 2021, NDLEA ta kama sama da tan bakwai na haramtattun kwayoyi da kudinsu ya haura Naira Biliyan 130 tare da gurfanar da mutane sama da 900 da ake zargi.

LABARAI MASU NASABA

DHQ Ta Ƙaryata Rahoton Yunƙurin Yi Wa Tinubu Juyin Mulki

‘Yansanda Sun Kai Samame Maboyar ‘Yan Ta’adda, Sun Kwato Miyagun Kwayoyi A Gombe

A nasa jawabin, Kwamandan NDLEA na shiyyar Sokoto, Kebbi da Zamfara, Muhammad Misbahu Idris, ya yabawa kokarin mai girma Sanata Abubakar Atiku Bagudu, da uwar gidansa Dakta Zainab Shinkafi Bagudu,  bisa gagarumin goyon baya da gudunmawar da suke bayarwa a Jihar Kebbi wajen ganin an magance matsalar na shan miyagun kwayoyi a fadin Jihar.

Haka kuma ya ce” yawaitar shaye-shayen miyagun kwayoyi a Nijeriya ya yi yawa, kafin yawan shan muggan kwayoyi a duniya ya kai kashi 15 cikin 100 amma a Nijeriya a yau ya kai kashi 15.

Haka zalika, ya yi kira ga iyaye da masu ruwa da tsaki da su zage damtse wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu wajen kula da ‘ya’yansu da kyau don kaucewa ga fadawa cikin shan miyagun kwayoyi ko kuma abokantaka da Matasa masu shaye shaye.

Bugu da kari, ya yi kira ga jami’an hukumarsa da su kara kaimi wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na kamawa da gurfanar da masu aikata laifin shan miyagun kwayoyi.

Tun da farko, kwamishinan ma’aikatar kiwon lafiya na jihar, Jafar Muhammad, wanda ya wakilci gwamnan jihar Kebbi, ya yi alkawarin ci gaba da bayar da goyon bayan gwamnatin jihar domin dakile ta’ammali da miyagun kwayoyi a jihar.

A wani bangare na bikin rana, an gudanar da atisayen tafiya da kafa da rera wakoki daga ofishin jiha zuwa fadar Sarkin Gwandu, daga nan sai suka zarce zuwa masaukin fadar shugaban kasa, inda aka gudanar da lakcoci kan shaye-shayen miyagun kwayoyi da laifuka, da kuma haramcin shan miyagun kwayoyi a cikin al’umma.

Mahalarta taron, sun hada da sakatare na dindindin na Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kebbi, Wakilan Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa, Hukumar Kula da Lafiyar Jama’a ta Tarayya, Jami’an Hukumar Kare Hadura ta Kasa, Jami’an Tsaro da Tsaron Farar Hula, Kungiyoyin Sa-kai da Kungiyoyin Jama’a.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tsadar Rayuwa Da Karuwar Ta’addanci Na Ci Gaba Da Tagayyara ‘Yan Nijeriya
Da ɗumi-ɗuminsa

DHQ Ta Ƙaryata Rahoton Yunƙurin Yi Wa Tinubu Juyin Mulki

October 18, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Adawa Da Dokar Ta-ɓaci A Ribas
Tsaro

‘Yansanda Sun Kai Samame Maboyar ‘Yan Ta’adda, Sun Kwato Miyagun Kwayoyi A Gombe

October 18, 2025
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja
Tsaro

Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

October 18, 2025
Next Post
Dole Ne A Ci Gaba Da Binciken Alkalin Alkalai Mai Murabus, Tanko Muhammad — Majalisa

Dole Ne A Ci Gaba Da Binciken Alkalin Alkalai Mai Murabus, Tanko Muhammad — Majalisa

LABARAI MASU NASABA

gombe

Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu

October 18, 2025
Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

October 18, 2025
An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

October 18, 2025
Tsadar Rayuwa Da Karuwar Ta’addanci Na Ci Gaba Da Tagayyara ‘Yan Nijeriya

DHQ Ta Ƙaryata Rahoton Yunƙurin Yi Wa Tinubu Juyin Mulki

October 18, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Adawa Da Dokar Ta-ɓaci A Ribas

‘Yansanda Sun Kai Samame Maboyar ‘Yan Ta’adda, Sun Kwato Miyagun Kwayoyi A Gombe

October 18, 2025
Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya

Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya

October 18, 2025
ASUU

Cikin Wata 9 Farfesoshi 309 Sun Bar Aiki A Jami’o’in Gwamnati, In Ji ASUU

October 18, 2025
Masanin Ilimin Physics Chen Ning Yang Ya Rasu Yana Da Shekaru 103

Masanin Ilimin Physics Chen Ning Yang Ya Rasu Yana Da Shekaru 103

October 18, 2025
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

October 18, 2025
Kasar Sin Ta Gargadi Amurka Game Da Yunkurin Samarwa Yankin Taiwan Makamai

Kasar Sin Ta Gargadi Amurka Game Da Yunkurin Samarwa Yankin Taiwan Makamai

October 18, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.