Makonni uku bayan tserewa daga gidan sa da ke Anguwan Makera, Kuta a karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja, wani kasurgumin mai safarar miyagun kwayoyi ga ‘yan bindiga, mai suna Mohammed Sani (Gamboli) ya shiga hannu.
Jami’an Hukumar NDLEA ne suka kama Gamboli a maboyar sa da ke jihar.
Jami’an NDLEA a ranar 20 ga Nuwamba, 2025, sun kai samame gidansa da ke Anguwan Makera, Kuta, bayan samun sahihan bayanai game da ayyukansa na miyagun kwayoyi, inda aka gano kilo 471.8 na tabar wiwi.
Kakakin NDLEA, Femi Babafemi, wanda ya bayyana hakan a ranar Lahadi, ya ce wanda ake zargin, wanda ya tsere a farmakin farko, jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ne suka bi sahunsa suka kama shi a daya daga cikin sansaninsa na miyagun kwayoyi a Anguwan Fadama, Kuta a ranar Alhamis 11 ga Disamba.
ADVERTISEMENT














