Fim din da aka yi shi da kagaggun hotuna mai suna “Ne Zha 2” ya zama fim din kasar Sin na farko da ya samu zunzurutun kudi har yuan biliyan 10, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 1.39 bisa jimillar kudadensa da aka samu a duniya, ciki har da na ba da sautonsa, inda ya zarce misalin da aka yi hasashe a ranar Alhamis, bisa bayanan da aka samu daga dandalin sayar da tikiti na Maoyan.
Wannan gagarumar nasarar da aka samu a rana ta 16 bayan fitowar fim din a ranar bikin sabuwar shekara ta kalandar gargajiya ta kasar Sin da ta kasance ranar 29 ga watan Janairu, ta shiga jerin ci gaban da fim din ke samu na kafa tarihi.
“Ne Zha 2” ya riga ya zama fim na farko da ya samu dalar Amurka biliyan 1 a kasuwa guda, sannan ya zama fim din da ba na masana’antar shirya fina-finan Amurka ba da ya shiga sahun masu kambun samar da kudin da ya kai dala biliyan.
Wasu manazarta da suka zanta da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a ranar Alhamis, sun bayyana cewa, sun yi imanin nasarar da “Ne Zha 2” ya samu ta zarce batun adadi mai kayatarwa da sashen fina-finan ya bayyana, inda take nuna matukar kuzari, da ban sha’awa, da kuma bajintar al’adun Sinawa da fikirarsu. (Abdulrazaq Yahuza Jere)