Hukumar agajin gaggawa ta ƙaasa (NEMA) ta ceto fiye da mutum 400 da ambaliyar ruwa ta rutsa da su a Maiduguri, Jihar Borno.
Mai kula da NEMA na shiyyar Arewa maso Gabas, Sirajo Garba ne ya bayyana hakan a yau Lahadi cewa tawagar hukumar ta agajin gaggawa (ERT) tana ci gaba da gudanar da aikin ceto.
- Gwamnatin Borno Ta Kafa Sansanin Kula Da Wadanda Ambaliya Ta Shafa
- Ambaliya: Gwamnatin Adamawa Ta Tallafa Wa Jihar Borno Da Naira Miliyan 50 Da Jiragen Ruwa 6
Bugu da ƙari, sashen kula da ceton gaggawa na NEMA, (MICU), ya kai ɗaukin taimakon duba marasa lafiya 171 a sansanonin daban-daban.
Domin magance ƙarancin ruwa, an tura tankar ruwa zuwa sansanin Fannami Gubio, inda ake shirin amfani da manyan motocin tsaftace ruwan sha. NEMA ta haɗa kai da Médecins Sans Frontières (MSF) wajen kafa cibiyoyin lafiya na wucin gadi, kuma tana aiki tare da hukumar kare muhalli ta Jihar Borno (BOSEPA) domin inganta tsaftar muhalli.
Haka zalika, a haɗin gwuiwa da ƙungiyoyin al’umma, NEMA ta raba kayan girki da kuma kafa asibiti don taimaka wa waɗanda ambaliyar ta shafa.