Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), ta karbi ‘yan Nijeriya 152 da suka dawo daga Kasar Libya ta filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas.
Ko’odinetan NEMA na shiyyar Kudu Maso Yamma, Ibrahim Farinloye ne, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.
- Shugaban Bankin Duniya: Sin Da Indiya Sun Tsallake Koma Bayan Da Tattalin Arzikin Duniya Zai Fuskanta A Bana
- Ma’aikatar Wajen Sin: Ba Sin Ce Ta Haddasa Koma Bayan Alaka Tsakanin Ta Da Amurka Ba!
Farinloye, ya ce mutanen da suka dawo sun taso ne daga Kasar Libya a cikin jirgin sama kirar Al Buraq Air Boeing 737-800 mai lamba 5A-DMG Buraq.
Wadanda abin ya shafa da suka isa filin jirgin sama na Legas, sun kunshi manya mata 54, manya maza 73 da yara.
Daga cikin wadanda suka tarbe su akwai Darakta-Janar na NEMA, Mustapha Habib Ahmed, tare da jami’an Hukumar Shige da Fice ta Kasa, Hukumar Hana Fataucin Bil Adama ta Kasa (NAPTIP), Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira, Hukumar Filin Jiragen Sama ta Tarayya da kuma rundunar ‘yan sandan Nijeriya.
Sanarwar ta kara da cewa, “Bayanan mutanen da suka dawo sun nuna cewa an dawo da mata manya 54, yara bakwai da jarirai mata uku.
“Haka kuma manya maza 73 da suka hada da masu fama da rashin lafiya, saj yara maza takwas da jarirai bakwai daga cikin rukunin.
“Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Duniya (IOM) da Ofishin Jakadancin Nijeriya a Libya, sun hada kai don taimaka wa ‘yan Nijeriya da suka makale bayan kokarinsu na tsallakawa tekun Bahar Rum zuwa Turai.”