Ofishin jakadancin Amurka a Nijeriya ya ce, ya tantance ‘yan Nijeriya fiye da 150,000 da suka hada da dalibai 30,000 da ke neman biza zuwa kasar Amurka a 2023.
Shugaban Ofishin jakadancin kasar Amurka, Mista David Greene ne ya bayyana hakan a ranar Lahadin da ta gabata yayin wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya a Abuja.
- Yadda Na Hana ‘Yan Boko Haram Mayar Da Jihar Neja Hedikwatarsu – Tsohon Gwamnan JiharÂ
- Donnarumma Ya Samu Katin Kora Bayan Minti 10 Da Fara Wasa.
Ya kuma ba da tabbaci ga masu neman biza zuwa kasar Amurka cewa, za a shawo kan duk wani kalubale da ake fuskanta kan neman bizar.
A cewarsa, “batutuwan da suka shafi biza za su zama tarihi, ofishinmu yana yin duk abin da ya kamata don ganin an shawo kan duk wani kalubale game da neman bizar.”
Ya bukaci masu sha’awar tafiya zuwa Amurka da su nemi bizar da wuri tare da tabbatar da cewa, bukatun da ke cikin bizar suna da alaka da tafiyar.