Arewacin Nijeriya, yanki ne mai cike da al’adu, tarihi, manyan biranai, wajen da tsoffin masarautu suka taba bunkasa kuma ayarin fatauci da kasuwanci suka bi, don ketarewa zuwa sahara.
Waiwaye adon tafiya! Tunawa da Daular Sakkwato da Masarautar Kanem-Bornu da Masarautar Kano da daukakar Sarauniya Amina ta Masarautar Zazzau da kuma labarin Daurama da Bayajidda, inda tarihi ya yi nuni da kyakkyawan yanayi na mulki, ilimi da kuma kasuwanci.
- Shugabannin Sin Da Rasha Sun Tattauna Da Juna
- Za A Bude Shafin Karbar Bashin Dalibai A Ranar 24 Ga Mayu
Ka da mu manta da abubuwan al’ajabi na gine-ginen yankin, gagarumar katangar Kano, Etsu Nupe da gudunmawar da suka bayar na fasaha, musamman a fannin fasahar sassaka ta terracotta. Mutanen Jukun da tsohuwar Masarautar Kwararrafa, ‘yan kabilar Berom wadanda suke da Sarkinsu na gargajiya a matsayin Gbong Gwom.
Har ila yau, al’adun Nok duk sun tsaya a matsayin shaida ga dimbin al’adun gargajiya wadanda suka dawwama shekaru aru-aru, a yanzu haka yankin na gaf da durkushewa; sakamakon rashin hadin kai, hangen nesa da kuma rashin sha’awar aiwatar da hadin gwiwa, ko shakka babu; hakan ya kawo cikas ga ci gabanta da kuma ci gaban al’umarta da samun zuwa ga nasarori na zahiri da ma’ana.
Bugu da kari, duk da karfin da yankin yake da shi da kuma dimbin albarkatunsa, yankin na fuskantar rudani wadanda suka hada da gwagwarmayar tattalin arziki, rarrabuwar kawuna, rashin shugabanci da gazawar shugabanci.
Wannan kasidan su ne, cikamakin kasidar da ta gabata mai taken ‘Waiwaye: Arewacin Nijeriya Sai Gamji Dan Kwarai’, da kuma jan hankalin yakin bisa jimillar Naira trillion 6, na kasafin kudin shekarar 2024.
A karshe, ga tambayar tiriliyan 6, shin akwai masu hankali da hangen nesa da ke kan karagar mulki ko neman hawan ta, wadanda za su iya rungumar ruhin sadaukarwa da kishin kasa, wanda a da ya ayyana yankin; don fitar da ita daga kangin da take ciki tare da kai ta ga hanyar zaman lafiya, jin dadi da kuma wadata?
Wane Ne Zai Iya Magana Da Yawun Arewacin Nijeriya?
Fitattun kungiyoyin da ke kare muradu da ci gaban yankin baki-daya, wadanda suka hada da Kungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa (NGF), Shugabannin Gargajiya da na Addini, Jama’atu Nasril Islam (JNI), Kungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN), Kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF) Kungiyar Magabatan Arewa(NEF), Gidauniyar Tunawa da Sir Ahmadu Bello, Gamayyar Kungiyoyin Arewa (CNG), Kungiyar Fadakarwa ta Arewa (NRF), Kungiyar Bincike da Ci gaban Arewa (ARDP), Gamayyar Arewa (NU), Kungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) da saauran makamantansu.
Wadannan majalisu da ke sama, na da halaye masu kama da juna guda uku; rashin hadin kai, rashin dabara da kuma rashin tsari, ta yadda za su tunkari kalubalen da ke addabar wannan yanki nasu, shi yasa ake yi musu kallon kamar tarin tsintsiya; amma babu shara.
Har ila yau, an gano gibi a cikin iyawar kungiyoyin; inda ayyukansu da tasirinsu ke cikin shakku, saboda rashin daidaituwar muradu daban-daban, rashin aiwatar da manufofin da aka tsara a matakin farko da kuma rashin isa ga al’ummomin yankin. Kazalika, kamar yadda muke sane da barazanar tsaro, garkuwa da mutane, rikicin manoma da makiyaya, rashin aikin yi da rikicin kabilanci da na addini, ya kasance mai muhimmanci ko hadari.
Annobar Almajiranci
Ilimi ginshikin rayuwa da ci gaba, ya kasance mafarki ga matasa marasa adadi, inda yankin ya kasance mai mafi yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a duniya, ciki har da almajirai marasa galihu, wadanda aka yi musu kaca-kaca da rayuwa ta fuskar kunci da rashin ilmin boko, yayin da shugabannin suka gwammace da yin taro a kasashen waje.
Mu dubi wasu kididdiga: Adadin kasafin kudi na shashen ilimi na Jihohin Arewa 19 a shekarar 2024, ya kai kimanin Naira biliyan 927.50, kamar yadda kasafin ya nuna.
Ziyara zuwa yanar gizo ta Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC), ta samar da lambobin jami’o’i kamar haka a watan Mayun 2024, yankin Arewa na da kusan jamiói 98 cikin 239 a fadin wannan kasa, wadanda suka hada da Jami’o’i masu zaman kansu 54, jihohi na da 10 ,sannan Gwamnatin Tarayya ta mallaki guda 34.
A cewar sanarwar Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF), wanda aka gabatar a Jihar Kano a watan Mayun 2022, “A Nijeriya, akwai yara miliyan 18.5 da ba sa zuwa makaranta, kashi 60 cikin 100 daga cikinsu ‘yan mata ne’’.
Rahoton da kungiyar ilimi ta Arewa maso gabashin Nijeriya ta fitar, na tsawon watan Afrilu zuwa Yuni 2023, a jihohin da rikicin ya shafa kamar Borno, Yobe da kuma Adamawa, akalla makarantu 802 sun kasance a rufe da ajujuwa 497 da aka lalata tare da wasu 1,392 da suka lalace, amma za a iya gyara su.
Bugu da kari, sauran kalubalen zamantakewar sun hada da talauci, bukatar rayuwa, rashin samun bukatun yau da kullum kamar abinci, matsuguni da kuma kiwon lafiya.
Shin Arewacin Nijeriya Na Fama Da Fatara?
Matsalolin basussukan da Jihohin Arewa ke fama da su da kuma fafutukar tattalin arziki, na kara nuna damuwa game da yadda ake tafiyar da harkokin kudi a yankin, inda jihohi da dama ke kokawa da dimbin basussukan, inda kuma dukkaninsu ke garzayawa Abuja da kokon bara; domin karbar tagomashi a madadin ‘yan kasarsu.
Idan aka kwatanta, da alama yankin yana cikin wani mawuyacin hali na tattalin arziki fiye da sauran sassan kasar. Ga takaitaccen bayani dangane da wannan batu:
A cewar Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS), kwamitin rabon asusun tarayya (FAAC) na watan Fabrairun 2024, kason Jihohin Arewa 19; Naira 164,340,391,889.67. Wadannan alkalumma na wakiltar adadin kudin da jihohin suka samu, bayan an cire kudaden biyan bashi da sauran wajibai na doka.
Alkaluma daga NBS na shekarar 2022, dangane da jimillar kudaden shiga da ake samu a cikin gida (IGR), na Jihohin Arewa 19, ya kama Naira biliyan 387.4.
Yayin da Ofishin Kula da Bashi (DMO) ya nuna jimillar basussuka ga Jihohin Arewa 19, kamar yadda a watan Disamba 2023 ya nuna shi ne, Naira 2,073,028,703,413.75, na bashin cikin gida da kuma na USD1,530,030,743.04 (Kimanin Naira biliyan 2,218,543,500,000, dangane da kimar ‘NAFED/NAFEM’ na 13 ga Mayun 2024; na bashin kasashen waje.
Alkaluman da ke sama, na da ban tsoro tare da nuna yiwuwar takura a cikin ikon yankin na samar da ayyukan raya kasa da kara saka hannun jari da ababen more rayuwa, kiwon lafiya, ilimi da sauran fannonin da ke haifar da ci gaban tattalin arziki.
Salon Rawar Wakilai Dangane Da Ayyukan Mazabu (Constituency Projects)
Bayanan NBS suna cewa, zuwa shekarar 2016; an kiyasta yawan mutanen Nijeriya miliyan 193.5, bisa kidayar hukumar yawan jama’a ta kasa (NPC), ta shekarar 2006. Jihohin Arewa na da mutane miliyan 100.9, Jihohin Kudu na da miliyan 89 da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja da ke da miliyan 3.56.
Tun daga shekarar 1960 zuwa yau, Arewa ta samar da shugabanni 10 daga cikin 16 da Nijeriya ta samu.
A Majalisar Dokoki ta Kasa, jimillar Sanatoci 109; 57 daga cikinsu wakilan Jihohin Arewa ne, sannan jimillar ‘Yan Majalisar Wakilai 360, Jihohin Arewa na da wakilai 191 daga cikinsu.
Duk da samar da adadi mai yawa na Shugabannin Kasa da kuma rike da kujeru masu yawa a Majalisar Dokoki ta Kasa, yankin ya shiga cikin tarkon da ba a taba tsammani ba da kuma tabarbarewar ci gaba. Muryoyin da ke fitowa ta cikin zaurukan mulki kamar suna watsewa kafin su iya kawo canjin da ake bukata.
Dalilan afkuwar wadannan abubuwa sun hada da rikice-rikicen cikin gida, tsoma baki, rashin kwarewa, son abin duniya, tasirin girman kai da kuma cin hanci da rashawa. Wadannan sun mamaye walwala da tsaro na mazabu da kuma dakile wakilci mai inganci.
Wasu misalai:
- A cikin rahoton nata, Budgit Tracka ta nuna cewa; a tsakanin shekarar 2009 zuwa 2019, an ware sama da tiriliyan 1 ga ayyukan mazabu a Nijeriya yayin da ta bibiyi ayyukan mazabu 15,859 a garuruwa 7,589 na Nijeriya a shekarar 2019. Sannan, ta bayar da rahoton kammala ayyuka 7,000 a fadin jihohi 26. Kazalika, ayyuka sama da 200 na biliyoyin Nairori aka yi watsi da su ko rashin kammalawa.
- Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (ICPC), ta yi zargin cewa; zababbun jami’an gwamnati sun karkatar da Naira biliyan 120 daga kudaden aikin mazabu na shekarar 2021.
- Misali na baya-bayan nan, na aikin mazabu da ya mamaye gari shi ne, a shiyyar mazabar Kano ta tsakiya; inda Dan Majalisar Dattawan ya ba da tukwane 500,000 na yumbu da farin alawayyo (Likkafani) 500,000, ga al’ummar mazabarsa; domin binne gawawwakinsu. Wannan ita ce Arewacin Nijeriya a yau!
Harkokin Kasuwanci Da Masana’antu
Fannin masana’antu na Arewacin Nijeriya, musamman a Kaduna, na nuni da tabarbarewar tattalin arziki; sakamakon rashin shugabanci na gari da rashin gudanar da ayyukan farfado da tattalin arziki da kuma fardado da masana’antu, wanda hakan ke haifar da tambayoyi game da makomar tattalin arzikin yankin gaba-daya.
Haka zalika, adadin matasan da ba su da aikin yi a jihohin Arewa 19 na da matukar yawa, wannan ya nuna rashin hangen nesa daga bangaren NGF da kuma rashin iya aiki daga bangaren NBS. Bayanan da take da shi kawai su ne ‘kashi 77.1 cikin 100, idan aka kwatanta rashin aiki zuwa yawan jama’a a cikin wata biyu na shekarar 2023’. Ina mamakin abin da hakan ke nufi!
Amma wata sa’a ga Jihohin Arewa 19, akwai rahoton ‘Forbes Ranking’ na shekarar 2021, wanda ya nuna kasancewar attajirai daga Arewacin Nijeriya a cikin sahun gaba a kima a duniya masu darajar arziki na Dalar Amuraka. Wadannan sun hada da:
Aliko Dangote, Abdulsamad Rabiu, Theophilus Danjuma, Mohammed Indimi da Sayyu Dantata da dai sauransu.
Duk da cewa, cin hanci da rashawa a gwamnati na iya hana wadannan ’yan kasa masu hannu da shuni kawo wa Arewacin Nijeriya dauki, amma fatanmu shi ne halin kirki, da’a da kishin kasa za su sa a yi nasara.
Tambaya Kafin Mu Kammala
Shin kuskure ne ko laifi a gaya wa masu madafun iko gaskiya?
Alhaji Adamu Rabiu ya rubuto daga Kaduna