Tauraron dan kwallon Brazil, Neymar Jr, na shirin zama babban dan wasan kwallon kafa na baya-bayan nan da zai koma gasar lig-lig ta kasar Saudiyya.
Bayan ya amince da kwantiragin shekaru biyu na komawa kungiyar Al Hilal daga kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint-Germain (PSG).
A yau litinin ne za a duba lafiyar tsohon dan wasan na Barcelona bayan ya amince ya kulla yarjejeniya mai tsoka na komawa Al Hilal.
Kuma ana sa ran za’a kammala cinikin nan da sa’o’i 48 masu zuwa.
Sky Sports ta ruwaito cewa PSG na shirin karbar kudi har fam miliyan 86.3 kan dan wasan na Brazil.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp