Hukumar kula da kwallon kafa ta Nijeriya ta sanar da ranar 20 ga watan Janairun 2024 a matsayin ranar da za a fara gasar cin kofin Federation na badi da ya kunshi karawa a tsakanin kungiyoyin jihohin kasar nan 36 na bangaren maza da mata.
A Talatar nan ne za a fara yi wa kungiyoyin jihohin da ke sha’awar shiga gasar rajista a babban birnin tarayya, Abuja.
- An Samu Hatsaniya Tsakanin Magoya Bayan Bayern Munich Da Galatasaray A Santanbul
- Gwamnan Zamfara Zai Binciki Badakalar Miliyan 774 A Hukumar Alhazai Ta Jihar
Hukumar ta tsayar da Naira dubu 150 a matsayin kudin rajistar kungiyar maza da kuma Naira dubu 100 a matsayin rajistar kungiyar mata, sai kuma Naira dubu 200, ga kungiyar da ta makara ba ta yi rajista akan lokaci ba a bangaren maza, sai Naira dubu 120 a bangaren mata.
A gasar ta bana dai kungiyoin Bendel Insurance da Bayelsa Queen a bangaren mata ne suka lashe gasar, wanda suka raba kyautar Naira miliyan 25 da aka bayar.
A bangaren mazan dai Bendel Insurance din ta doke Enugu Rangers da ci daya mai ban haushi a wasan karshe da suka buga, nasara irinta ta farko da suka samu tun shekaru 45 da suka gabata.
Yayin da a bangaren mata kuma Bayelsa Queens suka doke Rivers Angles da ci 4-2 a bugun daga kai sai mai tsaron raga da aka je, bayan da lokacin tashi daga wasan da ya cika babu kungiyar da ta yi nasara.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp