Nijeriya da tarayyar Turai (EU) sun tsara dabarun hikimomi na yadda za su yi amfani da damarmakin kimiyya da fasahar zamani da kirkire-kirkire ta hanyar bincike da ci gaba, domin ganin an hada karfi da karfe wajen samar da ci gaba mai ma’ana.
Wannan batutuwan na daga cikin muhimman abubuwan da taron ganawa a tsakani, wanda ministan kere-keren kimiyya da fasaha, Uche Nnaji da tawagar EU wanda Ambasadansu a Nijeriya kuma na ECOWAS, Samuela Isopi ya wakilta da aka gudanar a Abuja.
- Masu Zanga-zanga Sun Fito Duk Da Dokar Hana Fita A Jigawa
- Rahoton Zanga-zangar Yaƙi Da Fatara Da Tsadar Rayuwa A Nijeriya A Rana Ta 1
A jawabinsa, Nnaji ya ce kere-kere da bincike suna daga cikin manyan hanyoyin janyo ci gaba. Ya kara da cewa, ma’aikatar tasa ta himmatu wajen yin hadaka domin samar da hadin gwiwa da ganin an cimma nasarorin kai Nijeriya zuwa mataki na gaba.
Ya ce, “Ta hanyar kwarewa da kuma damarmakin abokan huldarmu wato Tarayyar Turai, za mu samu habaka ci gaban fasaharmu ta fuskacin da za mu iya shawo kan matsaloli da kalubalen da suke addabar yankunanmu. Bugu da kari, muna daukan matakin hadin gwiwa ta yadda za a kafa cibiyoyin kere-kere da kuma tallafa wa kanana da matsakaitan kamfanoninmu.”
Ya kara da cewa, zuba hannun jari a sashin bincike da ci gaba na matukar taimaka wa ci gaban tattalin arziki. Ya kuma kara da cewa, Nijeriya ta himmatu wajen ganin ta samar da yanayin da suka dace wajen cimma wannan nasarar.
“Ma’aikatarmu ta maida hankali wajen inganta kwazo da horas da ma’aikatanmu ta fuskacni kyautata kwazonsu da kuma zurfafa bincike ta hanyar kyautata alakarmu da cibiyoyin bincike na Tarayyar Turai. Azamar da muka sanya kan makamashi da binciken kimiya za su taimaka sosai ga kasashen nan biyu, Nijeriya da abokan hulda Tarayyar Turai.
“Shirye-shiryen Erasmus da kan inganta ilimi da musayar bincike a tsakanin Nijeriya da Tarayyar Turai. Mun sanya azama wajen kara yawan ‘yan Nijeriya da za su halarci wannan shirye-shiryen kuma za mu tallafa musu wajen samun cike damar samun gurbi. Wannan zai taimaka mana wajen ganin mutanenmu da suke da hazaka sun samu damar fadada saninsu da kuma gogewarsu,” ya shaida.
Jagoran tawagar EU a Nijeriya, Isopi, a jawabinta, ta lura da cewa cimma yarjejeniyar da Nijeriya ta yi da EU kan fasahar kimiyya da kere-kere a matsayin wani babban matakin cimma nasara. Ta kara da cewa, lamarin kimiyya da fasaha muhimman bangarori ne wajen samar da ci gaba kamar su makamashi, noma da kuma wadata kasa da abinci.
Ta ce, tuni EU ta fara taimaka wa Nijeriya wajen bunkasa bincike da kere-kere, tare da karawa da cewa, wasu tulin damarmakin ma suna tafe domin kyautata harkokin kimiyya da fasaha a Nijeriya.
Ita kuma a nata bangaren, babbar sakatariya a ma’aikatar kere-kere da fasaha, Esuabana Nko-Asanye, ta roki EU ne da ta horas da jami’an Nijeriya masu aiki a bangaren kimiyya da fasaha domin inganta musu kwazonsu da saninsu.