Zanga-zangar tsadar rayuwa da aka fi sani da #EndBadGovernance wacce aka shirya daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Agusta ta samu rashin armashi a rana ta uku a babban birnin tarayya Abuja.
A wani ɓangare na matakan da aka ɗauka don daƙile zanga-zangar, mahukuntan babban birnin tarayya (FCT) sun samu umarnin kotu da ya taƙaita masu zanga-zangar zuwa filin wasa na MKO Abiola. Masu shirya zanga-zangar sun buƙaci amfani da Eagle Square don taron su, amma an hana su shiga.
- Zanga-zanga: Kada Ku Mayar Da Kano Da Arewa Baya – Sanusi II
- Ta Kashe Mijinta Tare Da Babbaka Gawar A Abuja
A ranar farko, masu zanga-zangar sun nufi Eagle Square inda Ƴansanda suka tarwatsa su da hayaki mai sa hawaye bayan jurewa ta sa’o’i da suka yi. Jami’an tsaro sun sha wahala wajen shawo kan ƙungiyoyin da suka toshe hanyoyi suna tare da ƙona tayoyi a sassan Abuja yayin da zanga-zangar ta ci gaba cikin lumana a filin wasa.
A rana ta uku, ba a ga ko da mutum guda mai zanga-zanga ba a filin wasa na Abuja ba lokacin da jaridar Daily Trust ta kai ziyarar safiyar yau Asabar. Ƴansanda da Ƴan jarida dake filin wasa sun tsaya kawai suna kallon halin da ake ciki.
Da aka tuntube shi, ɗaya daga cikin masu shirya zanga-zangar ya bayyana cewa suna a tashar Berger, amma ba a ga masu zanga-zangar a can ba. Daga bisani mai shirya zanga-zangar ya bayyana cewa suna taron ɓullo da dabaru ne a cikin filin wasa.