Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Jihar Sakkwato, ya bayyana cewar akwai kalubale sosai a fannin samar da wutar lantarki a kasar nan wanda ya zama wajibi idan a na son samun ci gaba mai ma’ana a dauki gabaran matakai domin shawo kan matsalolin.
Ya ce fannin wuta na bukatar kwararru kuma gogaggun hannaye wadanda suke jajirtattu ta hanyar yin aiki da gaske domin shawo kan tarin manyan kalubalen da fannin ya jima yana fuskanta.
- Cristiano Ronaldo Ya Yi Watsi Da Karbar Albashi Mafi Tsoka A Duniya
- ‘Yansanda A Ebonyi Sun Damke Wasu Masoya Da Suka Sayar Da Jaririnsu A Kan Kudi N500,000
Ya ce Nijeriya za ta iya samun ci-gaba ne kadai a matsayin Kasa idan ta na da ingantacciyar wutar lantarki.
Ya ce kashe tsohuwar NEPA bai samu cikakkiyar nasara ba, har yanzu akwai kalubale sosai amma kuma za a iya shawo kan su idan Gwamnati da gaske take yi.
Gwamnan ya yi wannan bayanin ne a yayin da ya karbi bakuncin sabon Shugaban Hukumar Gudanarwar Kamfanin Wutar Lantarki na KAEDCO, Alhaji Abbas Muhammad Jega a Fadar Gwamnatin Sakkwato.
“Kasashe da dama sun yi, me zai hana mu ma mu yi? Ba za mu samu nasarar cika alkawulan mu ba, ba za mu gano damar da muke da ita ba idan ba mu gyara fannin wuta ba.” Ya bayyana.
Ya ce duk fannonin ci-gaba mafi yawa sun dogara ne ga samun wuta wanda a kan hakan ne ya ce Gwamnatinsa ta na goyon bayan bunkasa fannin wutar lantarki wanda a bisa ga wannan ne Gwamnatinsa ta kashe makuddan kudade wajen samar da na’urorin taransifoma da daga darajar layukan wuta a fadin Jihar.
Gwamnan ya bukaci Kamfanin da su rika amfani da tsarin lissafin kudin wutar da aka ci maimakon hasashe ba tare da lissafi ba.Ya ce ta hanyar sanya na’urar mita, hasashen kudin wuta da ake yi zai ragu sosai, wanda hakan zai sa a samu gagarumar nasara a kokarin da ake yi na bunkasa fannin samar da wuta.
Tambuwal wanda ya ce yin amfani da tsarin biyan wutar da aka sha, shine mafi dacewa kamar yadda kamfanonin sadarwa ke yi wanda jama’a ke jin dadin tsarin, don haka me zai hana a yi shi a fannin wuta?” gwamnan ya tambaya.
Ya ce yin hakan zai zama alfanu ga kamfanin domin za a gano kwastomomi na kwarai wadanda ke biyan wuta, haka ma wadanda ke biyan wuta za su gamsu kuma su ga alfanun biyan kudinsu kuma za rika cajinsu yadda ya kamata.
A jawabinsa Abbas Jega ya bayar da tabbacin cewar tattaunawar Kamfanin da Gwamnatin Jihar Sakkwato da jin bukatocin kwastomomin su ya karfafa fahimtar juna da samar da sakamako mai kyau a kakkarfan kamfani da samun wuta a kodayaushe a Jihar.
Ya kuma bayyana nauyin matsalolin da aka gabatar tare da bayar da tabbacin za su kara tashi tsaye wajen magance matsalolin tare da kara inganta bayar da hasken wuta da rage korafe- korafen jama’a.