Nijeriya da kasar Brazil sun sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna guda biyar domin inganta bangaren kasuwanci, diflomasiyya, kimiyya, sufurin jiragen sama da kuma hadin giwa a bangaren kudade.
Babban mashawarcin shugaban kasa kan yada labarai, Bayo Onanuga, shi ne ya sanar da wannan matakin a ranar Litinin. A cewarsa, Shugaban kasa Bola Tinubu ya yaba wa kokarin Shugaba Lula na sabunta kyakkyawar alaka a tsakanin kasashen biyu, ya nuna cewa har yanzu Nijeriya cike take da dimbin damarmakin da filayen da za su bai wa kamfanonin Brazil dama.
Shugaba Tinubu ya yi bayanin ziyarorin da ya kai kasar Brazil a baya wanda ya nuna gayar muhimmancin da ke akwai na kyautata alakar tattalin arziki a tsakanin kasashen.
Da yake fadada bayani kan bangarorin hadin gwiwar, Shugaba Tinubu ya nuna cewa Nijeriya a shirya take domin yin hadin giwa da kasar Brazil a bangaren musayar fasahohin zamani, wadata kasa da abinci, masana’antu, da kuma makamashi.
“Mun daukaka wannan alkawarin domin tabbatar da shi, kamar yadda kuka gani a cikin yarjejeniyar, ban san dalilin da ya sa masana’antar magunguna, wadanda Brazil ta yi zurfi da nisa a cikinsu ba za su iya kasancewa a Nijeriya ba.
“Ban ga dalilin da ya sa ba a raba fifikon fasaha na Brazil da Afirka ba. Mun tabbatar wa junanmu cewa mune kawai za mu iya bunkasa tattalin arzikinmu don taimakawa kasarmu,” Tinubu ya shaida.
Tinubu ya kuma bai wa masu zuba hannun jari tabbacin cewa manufofin farfado da tattalin arzikin Nijeriya na haifar da sakamakon masu kyau a halin yanzu.
“Sauye-sauyen da na dukufa samarwa tun lokacin da na hau kan mulkin Nijeriya suna matukar tasiri. Da farko sun yi tsanani, amma a halin yanzu ana ganin gayar sakamakon masu kyau,” ya tabbatar.
Shi kuma a bangarensa, shugaba Lula na Brazil ya nuna farin cikinsa ne da sake sabunta kyakkyawar alaka tsakanin Nijeriya da Brazil. Ya ce, a halin yanzu da duniya ta ci gaba, akwai bangarori da daman gaske da kasashen biyu za su iya amfanar junansu.
Ya ce kasashen biyu suna da damarmaki sosai na fadaka a matsayinsu na manyan kasashen a duniya da bakaken fata suka fi yawa, za su iya amfanar junansu musamman ta bangarorin noma, kiwo, mai da gas, taki, jirgin sama, bangaren kanikanci da sauran bangarorin da dama.
Bayan tattaunawar ta tsawon awanni biyu, shugabannin kasashen biyu sun shaida sanya hannun fahimtar juna da aka yi a Palácio do Planalto da ke Brasília.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp