Gamantin tarayya ta bayyana cewa, a halin yanzu tana bukatar Naira Tiliyan 55 domin cike gibe karancin gidajen da ake fama da shi a cikin shekara 10 masu zuwa.
Ministan gidaje da bunkasa birane, Arc. Ahmed Musa Dangiwa, ya bayyana haka a Abuja a yayin taron manema labarai abikin cikar ministan shekara daya a kan karagar mulki.
- Kakar Da Ta Fi Dacewa Da Noman Wake A Nijeriya
- Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Gidaje Fiye Da 200 A Kaduna – SEMA
Ya ce, a lokacin da suka dare karagar mulki shi da karamin Minista, Abdullahi Gwarzo, sun samar da tsare-tsare na bunkasa shirin samar da gidaje masu saukin kudi daidai da manufar Shugaban Kasa Bola Tinubu, ya ce wannan na da muhimmanci domin ‘yan Nijeriya su samu karin damar samun gidaje masu saukin kudi, wanda hakan zai taimaka wajen samar da walwala da kuma ci gaban tattalin arzikin kasa.
Ya kuma ce, domin cike gibin karancin gidaje a kasar nan, Nijeriya na bukatar a samar da akalla gidaje 550,000 a duk shekara nan da shekara 10, inda ake sa ran kashe naira tiliyan 5.5 a duk shekara.
“A binciken da aka gudanar, al’ummar Nijeriya sun kai mutum miliyan 220 ana kuma karuwa da kashi 2.5 a cikin dari, a kan haka ana bukatar gidaje 550,000 a cikin shekara 10 wanda ke bukatar Naira tiriliyan 5.5 domin aikin samar da gidajen”
“Duk mun san wadannan ba za su fito daga gwamnati ba kawai, akwai bukatar hada hannun da bangarorin kamfannoni masu zaman kansu domin cike wannan gibin, amma dole gwamnati ta samar da yanayin da ake bukata domin cimma wannan burin”.