• English
  • Business News
Saturday, May 24, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Nijeriya Na Da Karfin Tattalin Arzikin Sarrafa Kayan Dandanon Da Muke Bukata A Cikin Gida – Yahaya Yakubu

by Rabi'u Ali Indabawa
4 hours ago
in Tattaunawa
0
Nijeriya Na Da Karfin Tattalin Arzikin Sarrafa Kayan Dandanon Da Muke Bukata A Cikin Gida – Yahaya Yakubu
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

A cikin wannan hirar, Mataimakin Manajan ciniki da kasuwanci na, kamfanin AJINOMOTO, Yahaya Yakubu ya ce Nijeriya na da damar bunkasa samar da MSG na cikin gida, da sauransu.

Mece ce makomar samar da MSG a Nijeriya nan gaba?.

  • ‘Yan Adawa Na Cacakar APC A Yankin Arewa Maso Yamma Bisa Goyon Bayan Tazarcen Tinubu
  • ‘Yan Ta’adda Na Amfani Da Na’urorin Zamani Daidai Lokacin Da Sojoji Ke Da Karancin Makamai -Zulum

A halin yanzu, Nijeriya ba ta da kayayyakin more rayuwa domin samar da babban ma’aunin monosodium glutamate (MSG), muna da masana’antar tattara kaya ne kawai a Nijeriya. Ana samarwa ne da adanawa a Japan sannan mu tura shi ta Brazil, amma MSG iri daya da ake amfani da shi a Japan shi ne MSG din kuke ci a Brazil da Amurka. MSG kuma shi ne dai wanda ake sha a Nijeriya. Don haka, mu a nan muna yi ne daidai da yadda mutanenmu za su iya saya.

Nan gaba al’amura za su daidaita. Idan komai ya yi kyau, babu abin da zai hana mu samun masana’antar a Nijeriya saboda muna da albarkatun kasa. AJI-NO-MOTO® (MSG) ana yin shi ne daga karan sukari.

Hakan na nufin za mu iya samar da MSG a Nijeriya ba tare da shigo da kaya daga Japan ba?

Labarai Masu Nasaba

Ma’aikatar Kasuwanci Da Zuba Jari Ta Gudanar Da Bikin Makon Abokan Cinikayya

Yadda Na Juya Jarin Naira 15,000 Zuwa Babbar Harka – Safara’u

Na yi imanin za mu iya hakan

Kuma muna fasahar da za mu iya aiwatar da hakan?

Idan aka yi la’akari da albarkatun noma da Nijeriya ke da shi, musamman a cikin amfanin gona irin su rogo da rake, da kuma ta hanyar saka hannun jari kan ababen more rayuwa da fasahar kere-kere, akwai gagarumin yuwuwar bunkasa damar samar da MSG na cikin gida ta hanyar amfani da wadannan albarkatun kasa da ake samu.

Muna da injiniyoyi da yawa wadanda za su iya gyara injinan. Muna da dukkan abubuwan da ake bukata a Nijeriya don samar da kayan dandano. Yawanci muna samun abubuwan da duk da muke bukata. Idan kana bukatar ruwa mai yawa, muna da madatsun ruwa a Shiroro, Kaduna da Neja. Muna da filaye da yawa wadanda za su iya zama na noman rake. Idan ka je Adamawa, ana shuka rake.

Yawancin jihohin Arewa suna shuka rake kuma ana samun amfani da ingantacciyar. Tare da dabarun saka hannun jari da ci gaba, Nijeriya na da damar kafa nata wuraren samar da MSG, tare da yin amfani da albarkatu masu yawa na noma. Muna da karfin yin hakan.

An samu sabanin ra’ayi game da MSG a Nijeriya, wane hali ake ciki yanzu?

Tun kafin yanzu, ana samun hasashe marasa dadi. Amma sannu a hankali al’amura sun fara yin kyau. A halin yanzu, hasashe, da alama hasashen yana canzawa sannu a hankali, kuma mun fara ganinsa saboda karuwar sha’awar masu amfanin da abin.

Wace rawa kayanku ke taka wajen tallafa wa kasuwancin gida da ’yan kasuwa?

Cibiyarmu na raba kaya a fadin Nijeriya. Mun samar da tsarin a kamfanin domin raba kayayyaki wanda zai bai wa ‘yan kasuwar Nijeriya damar farawa da bunkasa kasuwancinsu. Ta hanyar ba da dama da rarraba samfuranmu a duk fadin kasar, ta hanyar ba da horo, da tallafin tallan da muke bayarwa, muna karfafa wa dillalai da kananan ‘yan kasuwa masu samar da kudin shiga da daukar wasu a cikin al’ummominsu.

Ta yaya kayayyakinku ke karfafa kanana da matsakaitan masana’antu (SMEs) ta hanyar sadarwa da rarraba ta?

Kamfaninmu yana hadin gwiwa tare da kanana da matsakaitan masana’antu (SMEs), kirkirar dama ga kasuwancin gida don bunkasa. Daga masu ba da kaya zuwa masu ba da ayyuka, ayyukanmu suna habaka kasuwanci, suna tallafa wa kirkirar ayyuka.

Ta wace hanya ce kayanku ke ba da gudunmawa ga abinci masu gina jiki?

Muna taka muhimmiyar rawa wajen habaka ilimantarwa, kwarewa, da ayyuka a cikin sassan kayan abinci masu gina jiki na Nijeriya, ta hanyar shirye-shiryenmu na koyar da abinci mai gina jiki da hadin gwiwar kwararrun masana kiwon lafiya. Ta hanyar yin hulda tare da al’ummomin likitoci da kimiyya, AJINOMOTO yana shirya tarurrukan karawa juna sani da bita don tattauna aminci da fa’idodin kayan abinci.

Ta yaya wannan alama ke tallafa wa samar da abinci da ilimin abinci mai gina jiki a Nijeriya?

AJINOMOTO yana ba da gudummawa sosai ga ingancin abinci da ilimin abinci mai gina jiki a Nijeriya ta hanyar tabbatar da amincin samfura da inganci, wannan shi ne muna ba da tabbacin mafi kyawun masana’antu da ayyukan samarwa. Har ila yau, ta hanyar ba da shawara don rage gishiri, mun gane abubuwan da ke tattare da lafiyar jiki mai yawa na sodium; don haka AJI-NO-MOTO® ya zama madadin mafi koshin lafiya ga gishirin gargajiya.

Za ka iya ba da tarihin wannan kamfani?

AJINOMOTO GROUP shi ne ya samar da AJI-NO-MOTO®, kayan dandano na umami na farko a duniya, wanda ya wanzu tun 1909, wato, sama da shekaru 100.

Mun himmatu wajen ba da gudummawa ga jin dadin dan’Adam, jin dadin rayuwar al’umma da jin dadin duniya tare da “Kimiyyar Amino”. An fara samar da AJI-NO-MOTO® a Nijeriya a shekarar 1991 tare da kafa kamfanin Ajinomoto Foods Nigeria Limited (AFN) wanda ya fara Sayar da Kayayyakin dandano na AJI-NO-MOTO® Umami a kasar tare da masana’antar shiryar kaya a Legas.

A yau, kamfanin ya fadada samfuran samfuransa daga MSG (monosodium glutamate), mashahurin AJI-NO-MOTO® zuwa kayan dandanon MaDish® da DeliDawa™. Kuma yanzu muna ci gaba da wasu samfurori. Don haka, kamfani ne da ke da kayayyaki iri-iri da ake nufi don biyan bukatun ’yan Nijeriya.

Wane irin kaso kasuwarku ke samu a masana’antar abinci ta Nijeriya?

Kasuwar Nijeriya wata kasuwa ce mai karfin gaske, wacce mutane ke da zabi daban-daban dangane da kayan dandano. Duk da rikitarwa,

Zan iya fayyace cewa muna sarrafa babban kaso na kasuwa a rukunin da muke taka rawa. Alamar yana da ginshiki mai karfi, kuma ya girma sosai a cikin kasuwar. Baya ga haka, muna da kayayyaki masu inganci. A halin yanzu, muna rike sama da kashi 70 na kasuwancin MSG a Nijeriya. Mantra na kamfani namu “Ku Ci Lafiya, Ku rayu lafiya” yana karfafa sadaukarwarmu don taimaka wa mutane su gina lafiya. Fiye da kowane lokaci, ko yaushe muna himmantuwa ga jin dadin rayuwar mutane, al’umma da duniya.

Ka yi magana game da bangaren kasuwanci, yaya game da masu amfani da kayan?

A cikin sanin yanayin masu amfani da shi, mun dage kan kirkira, sadaukar da kai ga ingancin samfuran, masu tsafta kuma hakan na ba mu damar yin gasa.

Mun ware samfura da muka mai da hankali kan kirkirar su da suka dace da al’adun dafa abinci na Nijeriya. Misali shi ne ci gaban DeliDawaâ„¢, kayan dandanon da aka shirya shi ta hanyar daddawar gargajiya. Wannan samfurin yana ba da dandanon gida. Muna daya daga cikin kananan kamfanoni a cikin nau’ikan kayan aikin da aka ba da cikakken tabbaci daga hukumar kula da tsaftar abinci kamar NAFDAC da SON.

 

Wadanne matakai ne kamfaninku ya bi don sauke wannan ilimi zuwa ga masu amfani, wajen ƙara ilmantar da su dangane da ayyukan CSR?

Muna da hadin gwiwar kungiyoyi da yawa, ciki har da gwamnati, tallafin kiwon lafiya, kungiyoyi masu zaman kansu da kungiyoyin ilimi da sauransu don fitar da ayyukan mu na CSR. Muna ilmantar da mutane ko dai ta hanyar hadin kai ko daukar nauyin aiki. A cikin ‘yan kwanakin nan, mun samar da ayyuka a fannin kiwon lafiya, ilimi, karfafa wa mata, tabbatar da tsaftar muhalli da dai sauransu.

 

Ta yaya kuke amfani da fasaha don tabbatar da samun samfurori masu inganci?

Muna mai da hankali kan bambance samfuranmu ta hanyar ba da sabbin abubwa mafi inganci. Wannan ya hada fasahar ci-gaba ko wasu fannoni na musamman wadanda suka tare da mu.

 

Idan kuna magana game da fasaha, wannan ci gaba ne na yau da kullum. Kowane lokaci muna hadin gwiwa don habaka ingantaccen aiki da ingancin samfuri, don haka muna ba da gudummawa ga daidaiton samfura. Misali, a farko, muna amfani da wasu injina wadanda ke da layika da suka samar da kayayyki nau’u biyu kawai. Mun kuma fadada shi zuwa kusan inji mai layi shida daidai da ka’idojin duniya.

 

Wane adadi kuke samarwa a duk shekara?

Saboda manufofin kamfani game da sirri, ba zan iya bayyana takamaiman alkaluman samar da kayayyaki ba, amma dai zan iya tabbatar maka cewa karfinmu ya yi daidai da bukatun kasuwa da hasashen ci gaba.”

 

Da yake ana magana ce game da yuwuwar DeliDawa, shin a zuciyarku kun taba tunanin fitar da wasu samfuran zuwa kasashe makwabta?

Bisa la’akari da yuwuwar ci gaban da ake samu a yankin kudu da hamadar sahara, tabbas muna da wani mutum da ke gudanar da harkokin kasuwanci zuwa kasashen waje. Kuma ta hanyarsa kadai, mun gabatar da DeliDawaâ„¢ da aka kai wasu kasashen Afirka kamar Guinea, Cote d’Iboire da Ghana. DeliDawaâ„¢ yana habaka bayanan dandano na asali daban-daban. Yanzu, yawancin wadannan kasashe sun zama babbar kasuwar kayan dandano. Ba abu mai sauki ba amma mun sami ci gaba. Kamar yadda ka sani, ba shi da sauki a fara sabon abu kuma ka girma cikin dan gajeren lokaci.

AJINOMOTO zai ci gaba da jajircewa wajen samar da samfura ta hanyar sadarwa mai yawa don karfafa kasancewarsu a kasuwannin Afirka.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Nijeriya
ShareTweetSendShare
Previous Post

Abin Da Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (2)

Next Post

Ƴan Bindiga Sun Kashe Mazauna Kauyuka 4 A Taraba Bayan Taron Zuba Jari

Related

Ma’aikatar Kasuwanci Da Zuba Jari Ta Gudanar Da Bikin Makon Abokan Cinikayya
Tattaunawa

Ma’aikatar Kasuwanci Da Zuba Jari Ta Gudanar Da Bikin Makon Abokan Cinikayya

7 months ago
Yadda Na Juya Jarin Naira 15,000 Zuwa Babbar Harka – Safara’u
Tattaunawa

Yadda Na Juya Jarin Naira 15,000 Zuwa Babbar Harka – Safara’u

7 months ago
Butulci Ya Yi Yawa A Siyasar Yanzu – Hon Dankaka
Tattaunawa

Butulci Ya Yi Yawa A Siyasar Yanzu – Hon Dankaka

9 months ago
Tuntuni Muka Yi GargaÉ—in Cewa, Zanga-zanga Za Ta Iya Zama Hargitsi – Minista Idris
Tattaunawa

Tuntuni Muka Yi GargaÉ—in Cewa, Zanga-zanga Za Ta Iya Zama Hargitsi – Minista Idris

10 months ago
Rashin Amfani Da Ilimin Taurari Ya Jefa Nijeriya Halin Da Take Ciki – Sheikh Muhajjadina
Tattaunawa

Rashin Amfani Da Ilimin Taurari Ya Jefa Nijeriya Halin Da Take Ciki – Sheikh Muhajjadina

10 months ago
Cika Shekara 100 A Duniya: Tarihin Shaikh Dahiru Bauchi Daga Bakinsa
Tattaunawa

Cika Shekara 100 A Duniya: Tarihin Shaikh Dahiru Bauchi Daga Bakinsa

11 months ago
Next Post
Ƴan Bindiga Sun Kashe Mazauna Kauyuka 4 A Taraba Bayan Taron Zuba Jari

Ƴan Bindiga Sun Kashe Mazauna Kauyuka 4 A Taraba Bayan Taron Zuba Jari

LABARAI MASU NASABA

Tsokaci Kan Yadda Wasu Matasa Ke Yin Aure Ba Tare Da Sana’a Ba

Tsokaci Kan Yadda Wasu Matasa Ke Yin Aure Ba Tare Da Sana’a Ba

May 24, 2025
Yadda Za Ki Hada Garin Sakwara

Yadda Za Ki Hada Garin Sakwara

May 24, 2025
Budurwa ƴar shekara 15 Ta Jefar Da Jariri A Sansanin Ƴan Gudun Hijira A Borno 

Budurwa ƴar shekara 15 Ta Jefar Da Jariri A Sansanin Ƴan Gudun Hijira A Borno 

May 24, 2025
NNPCL Ta Rufe Matatar Mai Ta Fatakwal

NNPCL Ta Rufe Matatar Mai Ta Fatakwal

May 24, 2025
Gyaran Jiki Da Kyawun Fata

Gyaran Jiki Da Kyawun Fata

May 24, 2025
Ƴan Bindiga Sun Kashe Mazauna Kauyuka 4 A Taraba Bayan Taron Zuba Jari

Ƴan Bindiga Sun Kashe Mazauna Kauyuka 4 A Taraba Bayan Taron Zuba Jari

May 24, 2025
Nijeriya Na Da Karfin Tattalin Arzikin Sarrafa Kayan Dandanon Da Muke Bukata A Cikin Gida – Yahaya Yakubu

Nijeriya Na Da Karfin Tattalin Arzikin Sarrafa Kayan Dandanon Da Muke Bukata A Cikin Gida – Yahaya Yakubu

May 24, 2025
Abin Da Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (2)

Abin Da Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (2)

May 24, 2025
Faduwar Jarrabawar JAMB Ta Tayar Da Bukatar Neman Sake Fasalin Hukumar

Faduwar Jarrabawar JAMB Ta Tayar Da Bukatar Neman Sake Fasalin Hukumar

May 24, 2025
Rashin Daukar Tsauraran Matakai Na Iya Durkusar Da Bangaren Noma – Shehu Galadima

Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci A Sama Wa Manoma Masu Renon Tsirrai Rancen Kudi

May 24, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.