Tawagar Nijeriya a karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, a babban taron bunkasa tattalin arzikn duniya ‘World Economic Forum (WEF)’ da ke guduna a garin Dabos, ta kasar Switzerland na fatan amfani ta dandamalin taron wajen nema wa kasar nan karin masu zuba jari, ministan harkokin kasashen waje, Ambasada Yusuf Tuggar, ya bayyana haka a tattauwarsa da manema labarai.
Ana sa ran halartar shugabannin kasashe fiye da 52 ciki har da shaugaban kasar Chana Di Jinping, da shugaban kasar Jamus Olaf Scholz, tare da shugabanin manyan kamfanonin duniya fiye da 1,500. Wannan shi ne taro karo na 54, taron kuma zai fara ne daga ranar 15 zuwa 19 ga watan Janairu 2024.
- Jihar Kaduna Za Ta Ƙarfafa Ƙawancen Tattalin Arziki Da Ƙasar Jamus
- ‘Yansanda Sun Cafke Wasu Mutane Biyu Da Ake Zargi Da Satar Keke-napep A Kano
Cikin manyan-manayan abubunwa da za a tattauna a taron sun hada da yadda za a farfado da tattalin arzikin duniya, wanda kuma wannan na daga cikin akiblar da Nijeriya ke fuskanta a karkashin shugabancin Shugaban Kasa Bola Tinubu.
Ministan ya kuma bayyana cewa, halartar Nijeriya a taron yana da matukar muhimmanci ga tattalin arzikin kasa. Musamman ganin akidar shugaban kasa na ‘Renewed Hope Agenda’ na samar da aikin yi ga matasanmu da kuma tabbatar da sdoka da oda.
Ambasada Tuggar ya kuma lura da cewa, babban makasudin taron shi ne samar da mafiya ga mastalolin tattalin arzikin da al’ummar duniya ke fuskianta.
Ana kuma sa ran mataimakin shugaban kasa Shettima zai jawo kan masu zuba jari na su shigo don zuba jari a bagarorin tattalin arzikin Nijeriya, tare da sanar da su garabasar da gwamnatin Tinubu ta tanada ga musu zuba jari.