Wasu jami’an gwamnati da na kamfanoni, sun bayyana sama da kashi 70 cikin dari na al’ummar kasar nan a matsayin wadanda suka dogara da fannin aikin noma, sai dai abin takaicin shi ne, Nijeriya na fuskantar kalubalen rashin wadatattun kayan aikin noma na zamani, wanda hakan ke jawo wa fannin aikin noman koma baya.Â
Wata kididdiga da bankin duniya ya yi a kan harkar aikin noman a kasar nan, ya tabbatar da cewa; taraktocin da Nijeriya ta mallaka don yin noma bai haura 45,000 kacal ba, mai makon akalla guda 81,000 don aiwatar da harkokin noman.
- Gwamna Uba Sani Ya Kafa Kwamitin Binciken Matsalolin Aiki Hajji
- Basirar Henry Kissinger Abu Mai Daraja Ne Ga Amurka
Haka zalika, yanzu haka a kasar nan akwai akalla famfunan ban ruwan noman rani sama da 200,000 da sauran makamantansu.
Sannan, Nijeriya na da fadin kasar noma kuma ingantacciya kimanin 8,000, wanda hakan ke nuna cewa; kasar na da kimanin kadadar noma kimanin miliyan 80.
Bugu da kari, a cewar wani rahoton bankin duniya, bangaren gwamnati na shigo da akalla kashi 90 a cikin 100 na taraktocin noma cikin kasar nan, wanda kuma Ma’aikatar Aikin Noma da Raya Karkarar ce ke karbar wannan adadi, sannan mafi akasarinsu, kananan taraktoci ne.
Kazalika rahoton ya kara da cewa, bangaren kamfanoni masu zaman kansu, na shigo da taraktoci zuwa cikin kasar nan akalla kashi 10 cikin 100 a duk shekara.
Har ila yau, wadannan taraktocin noma na kai wa tsawon shekaru bakwai kafin su daina aiki, amma ya danganta da irin yadda samfurin taraktar ya ke.
Wakazalika, an kiyasta cewa sama da taraktocin noma 200 ne ke daina aiki duk da cewa, a duk shekara ana shigo da kimanin 1,000 Nijeriya.
Sai dai, domin kokarin lalubo mafita a kan karancin taraktocin, a kwanakin baya, Ma’aikatar Aikin Noma da Samar da Wadataccen Abinci, ta kulla yarjejeniya da kamfanin John Deere da ke kera taraktoci, domin samar da akalla taraktoci 2,000 ga wannan kasa, musamman domin a kara bunkasa fannin aikin noma na zamani.
Haka nan, ana sa ran wannan yarjejeniya da aka kulla; za ta kai tsawon shekaru biyar, wanda a karkashin yarjejeniyar za a samar wa Nijeriya taraktoci 10,000.
Ministan Aikin Noma da Samar da Abinci, Sanata Abubakar Kyari ya bayyana cewa, Nijeriya na fuskantar matukar karancin kayan aikin noma na zamani.
Kyari ya kara da cewa, ma’aikatarsa ta kulla yarjejeniya da kamfanin kera taraktoci na John Deere, domin samar da taraktoci sama da 2,000 a kan farashi mai sauki, don hakan ya bai wa kananan manoma samun damar siya a fadin wannan kasa baki-daya.
A cewar tasa, an samu damar kulla wannan yarjejeniya ce, biyo bayan wata ganawa a kwanakin baya da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima ya yi da wasu manyan jami’ai na Kamfanin John Deere a Kasar Amurka.
Wannan yarjejeniya, za ta kuma bai wa Kamfanin John Deere da abokan hadakar damar kafa masana’antar hada taraktoci a kasar nan, wadda bayan an sayi taraktocin; za kuma a dangana da su ga manoma kai tsaye.
Wakazalika, kwararru a fannin aikin noma a kasar nan, sun yi fatan dorewar wannan yarjejeniya, musamman ganin Ma’aikatar Aikin Noma a baya ta sha kulla ire-iren wannan yarjejeniya; amma sai ta gaza cimma burin da ta sanya a gaba.
Mista Jason Brantley, Mataimakin Shugaba a Kamfanin John Deere, ya bayyana jin dadinsa na shirin kafa kamfanin hada taraktocin noma a kasar nan.
Brantley ya sanar da cewa, kamfanin ya mayar da hankali ne wajen lalubo da mafita a kan kalubalen da kananan manoma ke fuskanta tare da habaka aikin noma da kayan aiki na zamani.
A cewarsa, Kamfanin John Deere ya mayar da hankali ne a kan yin noma da kayan aiki na zamani, domin aiwatar da aikin na noma mai tarin yawa a kadadar noma tare da kara bunkasa samar da wadataccen abinci a fadin kasar nan baki-daya.