Rahotanni sun nuna cewa Nijeriya na iya fuskantar ƙarancin mahajjata a bana sakamakon tsadar kujerar hajji, kamar yadda hukumar NAHCON ta bayyana.
A ranar Litinin, NAHCON ta sanar da sabon farashin kujerar hajjin bana wanda ya kai kimanin Naira miliyan takwas da rabi a wasu yankuna, kuma ya fi haka tsada a wasu wuraren.
- An Watsa Shirin Fadakarwa Na Shagalin Murnar Bikin Bazara Na CMG A Masar
- Ana Sa Ran Bude Sabon Babin Raya Dangantakar Sin Da Amurka
Wannan ya jawo damuwa sosai a tsakanin maniyyata.
Yanzu haka, da ya rage ƙasa da wata guda kafin wa’adin kammala biyan kuɗin aikin hajjin bana, alamu sun nuna cewa mutane da yawa ba za su iya biyan kuɗin ba.
Wannan na iya sa hajjin bana zama wanda Nijeriya za ta tura mafi ƙarancin mahajjata.
Farashin da NAHCON ta fitar ya nuna cewa:
- Maniyyata daga Kudancin Nijeriya za su biya Naira miliyan 8 da dubu 700.
- Maniyyata daga Arewa maso Gabas za su biya Naira miliyan 8 da dubu 300.
- Maniyyata daga sauran Arewa kuma za su biya Naira miliyan 8 da dubu 400.
Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya bayyana cewa an yi iyakar ƙoƙari don rage farashin kujerar daga kai wa Naira miliyan tara.
A baya, an yi tsammanin farashin zai iya kai har Naira miliyan 10 saboda karyewar darajar Naira.
Dokokin NAHCON sun bayyana cewa duk wanda bai kammala biyan kuɗin aikin hajjin kafin ranar 5 ga watan Fabrairu ba, ba zai samu damar tafiya hajjin bana ba, sai dai ya jira zuwa shekara mai zuwa.