Gwamnatin Tarayya na shirin samuun kimanin Naira tiriliyan 6.99 a matsayin kudin shiga a duk wata daga fannin mai.
Wannan na zuwa ne, daidai kamfanin albakatun man fetur na kasa NNPCL, ya yi hadaka da masu ruwa da tsaki, suka kara kudin sarrafa danyen mai zuwa Ganguna miliyan 1.8 a duk wata.
- Dan Nijeriya Lookman Na Kan Gaba Wajen Lashe Kyautar Gwarzon Kwallon Kafa Na Afrika Ta Bana
- ‘Yan Majalisar Nijeriya Na Matsin Lamba Ga Jami’an Gwamnati Wajen Yin Cushe A Kasafin Kudi –Jega
Farashin samfarin danyen mai na Brent duniya a 2024, ya kai kimanin Ganguna 81 a 2024.
Wannan ya kai kasa da farashin kowacce Ganga daya a kan 101 a 2024, idan aka kwatanta da farashin kowacce Ganga daya a akan dala 82 a 2023.
Samar Ganugunan mai miliyan 1.8 wanda ya kai dala 81 na kowacce Ganga daya, Nijeriya za ta samu kudin shiga da suka kai dala miliyan 145.8, wanda hakan ya nuna cewa, a cikin kwanuka 30, ya kai dala biliyan 4.37.
A tsakatsakin kudin musaya a hukumance na Naira 1,600, hakan ya kai Naira tiriliyan 6.99, wanda aka kiyasta Gwamnatin za ta samu a wata saboda karin farashin man na kwananan.
Shugaban Kamfanin NNPCL, Mele Kyari, ne ya sanar da karin a wata ganawa a shalkwatar kamfanin a ranar Alhamis a Abuja.
Karamin ministan albarkatun mai Heineken Lokpobiri, ne ya jagoranci ganawar, inda kuma ganawar ta samu halartar shugaban hukumar NNPCL Cif Pius Akinyelure Akinyelure.
Kazalika, babban mai kula da kudade Mista Adedapo Segun, da shugaban sashen hako mai na cikin ruwa Isiyaku Abdullahi, da mataimakin hako mai na kan tudu Udobong Ntia da na sashen zuba hannun jari a man ake hakowa a kan tudu Mista Bala Wunti da sauransu, duk sun halaci ganawar.
A lokacin ganawar da aka yi a watan Disambar 2023 da kwamitin kula da kudi na majalisar tarayya Mele Kyari ya bayar da tabbacin cewa, hasashen da ka yi na samar da danyen mai da farashin sa a cikin kasafin kudi na 2024, abu ne da yake mai yuwuwa.
Kazaliuka, kamfanin ya sanar da cewa, a yanzu yana samar da iskar Gas da ya kai biliyan 7.4, musamman na AKK.
Wannan ya kasance an samu ci gaba na samar da iskar Gas din da ta kai biliyan 6.1 a farkon 2024.
A jawabinsa a wajen ganawar babban jami’I a NNPCL lawal Musa ya sanar da cewa, bisa wannan hadakar da mahukuntan na NNPCL suka yi da masu ruwa da tsaki a fannin mai, musamman abokan huddar kamfanin da gwamnati da hukumomin tsaro masu zaman kansu da alumomi, hakan ya taimaka wajen cimma burin da aka sa a gaba.
Lawal ya sanar da cewa, “ Hakan ya sanya a yau, ake tunkahu da masana’antar domin mun ji dadi matuka duba da cewa, mun zarce wajen hako Ganguna miliyan 1.8 a duk rana daya.”
A cewarsa, wannan babbar nasara ce da aka samu tun bayan tsawon lokaci da ba a samu ba, amma mun samu nasarar cimma haka a yanzu.
Ya kara da cewa, a yanzu har ta kai gam un haura samar da iskar Gas da ta kai 7.4, wannan ba karamar nasara bace, inda ya kara da cewa, NNPCL ya mayar da hankali don samar da Gangunan danyen mai da suka kai miliyan biyu a karshen shekara.
A cewarsa a ranar 25 ga watan Yunin a lokacin da aka fara hako danyen mai bai wuce Ganguna 1.430 ba amma a ranar 11 ga watan Agusta, ya karu zuwa Ganguna 1.7
Ya sanar da cewa, wannan nauyi ne da Gwamnatin Tarayya ta dorawa kamfanin na cewa, dole ne hako