• English
  • Business News
Saturday, July 19, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Nijeriya Na Kashe Naira Miliyan 4.3 A Kullum Don Ciyar Da Wadanda Ke Jiran Hukuncin Kisa

by Idris Aliyu Daudawa and Sulaiman
4 hours ago
in Rahotonni
0
Fyade
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Gwamnonin Nijeriya ba su amince da sanya hannu kan hukuncin kisa ga wadanda aka yanke wa hukuncin kisa, kamar yadda wani bincike da LEADERSHIP Weekend ta gudanar inda ya nuna cewa gwamnatin tarayya na kashe Naira miliyan 4.3 a kullum don ciyar da fursunoni 3823 da aka yankewa hukuncin kisa.

Sakamakon haka, adadin fursunonin da aka yankewa hukuncin kisa a Nijeriya ya kai 3,823 a watan Yunin 2025.

Masana sun ce wadannan fursunonin sun ci gaba da kasancewa a sarka a cikin wani yanayi na doka: an yanke musu hukuncin kisa amma ba a kashe su ba, an bar su da rai, amma tsarin shari’a ya manta da su.

LEADERSHIP Weekend ta nakalto cewa yayin da aka zartar da hukunci na karshe, an jibge wadannan mutane da dadewa cikin gidajen yari masu cunkoso, cikin tsarin da ke haifar da damuwa mai zurfi da gurbatar dabi’a.

Hukumar Kula Da Gyaran Hali ta Nijeriya (NCoS) ta tabbatar da cewa daga cikin fursunoni 3,823 da aka yanke musu hukuncin kisa, 3,742 maza ne, 81 kuma mata ne, wanda adadain ya karu daga 3,688 a watan Maris na 2025 da 3,590 a watan Satumban 2024.

Labarai Masu Nasaba

2027: Gangamin ‘Yan Adawa Ya Sa APC Fafutukar Neman Mafita

Na Shiga Aikin Soja Domin Gujewa Yin Auren Fari Da Ƙuruciya — Buhari

Ai wannan bai ma zama labari ba, cewa duk da karfin da tsarin mulki ya bai wa gwamnonin jihohi na ba da izinin aiwatar da hukuncin kisa ko sassauta hukuncin, ba kasafai ake yanke irin wannan hukunci ba.

Bayanan da LEADERSHIP Weekend ta samu daga wani babban jami’i a ma’aikatar harkokin cikin gida, ya nuna cewa, jimillar fursunonin Nijeriya, ciki har da 78,446, Gwamnatin tarayya na kashe kimanin Naira miliyan 58.8 wajen ciyar da su a kullum.

Ya zuwa wannan lokaci, an ware wa kowane fursuna kudin abinci Naira 750 a kullum, adadin da ake ganin ya yi kadan. Duk da haka, bayan zanga-zangar da kuma kiraye-kirayen da aka yi ta yadawa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kara kudin zuwa Naira 1,125 a watan Agustan 2024 na fursunonin da suke jiran shari’a.

Wasu masu ruwa da tsaki da wasu manyan jami’an gidan yari da suka yi ritaya wadanda suka nemi a sakaya sunayensu sun shaida wa LEADERSHIP Weekend cewa, ko da za a kimanta sama da Naira 1,125 ba za ta kai kimanin Naira1,346 da ake bukata don cin abinci na yau da kullum ba, wanda hakan nuna an cire Naira 221 da ya gaza samar da abinci mai gina jiki ga kowane fursuna, gibin da masana gidan yari ke yi da ka iya haifar da mummunar illa.

“Rashin ciyarwa na iya haifar da tashin hankali,” in ji wani babban jami’i a wani gidan gyaran hali da ya shaida wa wakilinmu ta wayar tarho.

“Wannan lamari bai fa tsaya kan ba batun jin dadin jama’a ba; abin da ya shafi tsaron kasa ne,” in ji shi, ya kara da cewa abinci mai gina jiki da dabi’un fursunoni suna da alaka da juna.

Wani daftari na musamman da LEADERSHIP Weekend ta samu ya nuna yadda l’amuran kasafin kudi ke ba da mamaki.

Tsakanin Janairu da Fabrairun 2025, NCoS ta kashe Naira biliyan 3.3 don ciyar da fursunoni kusan 50,000 da ke jiran shari’a a cikin watanni biyu kacal. Tare da ciyar da fursunoni 50,000 akan Naira 1,125 a kullum, kudin da aka kiyasta zai kai Naira biliyan 20.6 a duk shekara.

Gaba daya, NCoS ta yi kasafin Naira biliyan 38 don kayan abinci a cikin 2025 kadai, tare da wadanda aka yanke hukuncin kisa a cikin wannan rabon, kodayake ba a kididdige kudaden su daban ba.

Wani kwararre kuma tsohon dan kwangilar samar da abinci a gidan yarin Kuje, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce, “Duk da kashe kudi, abincin da ake kashewa a gidan yari bai isa ba, alawus din yau da kullum ba ya hada da lafiyayyen abinci, dole ne gwamnati ta dauki ciyar da fursunoni a matsayin wani bangare na tsare-tsaren tsaron kasa.

Da yake magana kan kin sanya hannu kan sammacin kisa da gwamnonin suka yi, lamarin da ke ci gaba da rura wutar rikicin, wani mai rajin kare hakkin dan’Adam Esor Ekpe ya yi ikirarin cewa wannan ra’ayi, ko sanya hannu, ana amfani da shi ne ba bisa ka’ida ba, kuma hakan yana damun fursunonin ciki.

“Tun lokacin da mulkin dimokuradiyya ya fara a 1999, ba kasafai ake aiwatar da hukuncin kisa ba. Babban tashin hankali da aka fara gani shi ne abin da aka gani a karkashin mulkin Janar Sani Abacha, kisan fitaccen dansanda Ken Saro-Wiwa a 1995 gami da aka rataye ‘Ogoni Nine.’ Abubuwa kadan ne kawai suka faru a shekarar 2013 da 2016 na laifuka da ba a dauki mataki ba, wanda kuma ta hakan ne hukuncin kisa ya ci gaba da tabrarbarewa.”

Ekpo ya jaddada cewa hukuncin kisa yana da nasaba da sa hannun gwamnoni.

“Su ke, rike da kukamai amma da yawa sun zabi kada su yi amfani da hukuncin kisa.”

Sai dai hukumar da ke kula da gidajen gyaran hali ta Nijeriya ta yi zargin cewa rabon ciyarwar, duk da takurar da ake ciki ya ci gaba da kasancewa daidai da ka’idojin kasa da kasa da kuma dokokin cikin gida.

Mai magana da yawun hukumar gyaran hali ta kasa (NCoS), mataimakin Konturola Umar Abubakar, ya shaidawa LEADERSHIP Weekend cewa tsadar ciyar da fursunoni a Nijeriya bai wuce kima ba idan aka yi la’akari da halin da tattalin arzikin kasar ke ciki.

Ya kuma bayyana cewa, hukumar tana aiki ne a karkashin kasafin kudin da gwamnatin tarayya ta amince da shi, inda ya ce rabon da ake bai wa kowane fursuna ya yi kadan ya tabbatar da cewa fursunonin sun samu mafi karancin abincin da ake bukata kamar yadda ka’idojin kasa da kasa da ka’idojin cikin gida suka tsara.

“Yana da muhimmanci ga jama’a su fahimci cewa abinci shi ne ainihin tanadi ga daidaikun mutane da ke tsare, wadanda yawancinsu suna jiran shari’a kuma tsarin mulki ya dauka ba su da laifi.

Umar ya kara da cewa ayyukan da ake yi suna tabbatar da cika mafi karancin ka’idojin abinci mai gina jiki daidai da ka’idojin duniya da na cikin gida.

“Wannan tanadi ne na yau da kullum ga mutanen da ke tsare, wadanda yawancinsu har yanzu suna jiran shari’a kuma ana dauka cewa ba su da laifi a karkashin doka. Bugu da kari, wannan aikin na kokarin neman hanyoyin inganta ayyukan noma a cikin cibiyoyin tsare-tsare da wuraren aikin gona.

“Wadannan yunkurin suna nuna sadaukarwar aikin ga alhakin kasafin kudi, gyare-gyare, da kuma kula da mutuntaka ga duk mutanen da ke tsare, daidai da mafi kyawun hanyoyin gyara na kasa da kasa,” in ji shi.

Ya kuma tabbatar da cewa a halin yanzu Hukumar Kula da Gyaran Hali ta Nijeriya (NCoS) tana kashe Naira 1,125 ga kowane fursuna a kowace rana wajen ciyar da su, biyo bayan karin kashi 50 cikin 100 daga kudin farko Naira 750 da aka aiwatar a watan Agustan 2024 bisa umarnin shugaban kasa.

A halin da ake ciki, tsarin gwamnatin tarayya na gyaran hali ga alama yana canzawa. Ministan cikin gida a baya ya jaddada cewa “cibiyoyin gyaran hali a yanzu su ne wuraren bege da canji,” yana mai nuni ga tsoma baki kamar kara yawan alawus, kokarin gina fasaha, da kuma kaddamar da dakunan karatu na dijital ne suka sanya hakan.

Duk da haka, masana sun yi gargadin cewa, muddin ba a dauki kwararan matakai ba, gami da kawar da koma baya na aiwatar da kisa da kuma samar da isassun kudade na abinci mai gina jiki, gidajen yari na iya zama matattarar tarzoma.

 

Jinkirta hukuncin kisa saboda daukaka kara

Wani kwararren lauya mazaunin Bauchi Barista Sufiyanu Gambo Idris, ya bayyana cewa rashin aiwatar da hukuncin kisa a Nijeriya ya samo asali ne sakamakon tsawaita daukaka karar da gwamnonin jihohi suka yi na siyasa.

Da yake zantawa da LEADERSHIP Weekend kan wannan batu, Idris ya bayyana cewa mafi yawan hukunce-hukuncen kisa suna samuwa daga kananan kotuna da manyan kotuna da kotunan shari’ar Musulunci.

Ya jaddada cewa wadanda aka samu da laifi a irin wadannan shari’o’in na da ‘yancin daukaka kara a kotun kolin kasar, matakin da ke kawo tsaiko na tsawon shekaru.

“Har sai kotun daukaka kara ta karshe ta tabbatar da hukuncin, don haka ba za a iya aiwatar da hukuncin kisa ba,” in ji shi.

Idris abin ya fi kawo cikas na shari’a shi ne, rashin amincewar gwamnonin jihohi na sanya hannu kan sammacin kisa ya zama wata babbar matsala.

Ya kara da cewa, “Ko da duk wata hanyar doka ta kare, gwamnonin da tsarin mulki ya tanada su ba da izinin aiwatar da hukuncin kisa, galibi ba su da niyyar yin haka,” in ji shi.

 

Babu wani gwamnan Akwa Ibom da ya sanya hannu akan hukuncin kisa tun 1999

Tun daga 1999 da aka fara muliki siyasa babu wani zababben gwamna da ya rattaba hannu kan hukuncin kisan da aka yanke wa fursunoni a Jihar Akwa Ibom.

Wani babban jami’in Hukumar DPP da ya nemi a sakaya sunasa ne ya bayyana haka ga LEADERSHIP Weekend.

A cewarsa, a fadin gidajen yari hudu da ke Uyo, Eket, Ikot Ekpene da kuma Ikot Abasi, “muna da fursunoni da dama da aka yanke musu hukuncin kisa, amma ba za mu iya tantance adadinsu ba a yanzu saboda yadda wasu fursunonin da aka yanke musu hukuncin kisa ba da dadewa ba aka sake su bayan an sake duba shari’arsu a kotun daukaka kara domin gano cewa an samu kuskure wajen samunsu da laifi.”

“Kamar yadda ta faru kan wani mutum da aka yanke wa wani mutum dan Karamar Hukumar Ibesikpo Asutan hukuncin kisa bisa laifin kashe dan uwansa bisa zargin yin amfani da sihiri a babbar kotun Uyo.

“Da kuma wani misalin, wasu ‘yan asalin Karamar Hukumar Mkpat Enin, wadanda alkalin ya yanke musu hukuncin kisa bisa kuskure bayan da wani mugun mutum daga kauyensu ya jefe su da zargin hannu a garkuwa da mutane, an sako su bayan shekaru 12 suna jiran kisa.

‘Allah ya shiga lamarinsu, domin an sake su makonnin da suka gabata bayan sun shafe sama da shekara 12 a gidan yari suna jiran a zartar musu da hukuncin kisa biyo bayan daukaka kara da wani nagartacce ya yi a Kotun Daukaka Kara saboda wadanda ake zargin ba su da karfin daukaka kara.

“Don haka, shi ya sa ba za a iya tabbatar da sahihancin adadin wadanda aka yankewa hukuncin kisa a Akwa Ibom ba, saboda har wasu ake canjawa wuri wasu lokutan a wajen jihar,” in ji shi.

Sai dai wata majiya da ke kusa da gwamnan ta ce, “Wasu gwamnonin sun gwammace wadanda aka yanke wa hukuncin su dawwama a gidan yari maimakon kashe su.”

 

Matsin lamba ga gwamnatoci ta hanyar bin yarjejeniyar kasa da kasa

Baya ga haka, ya lura cewa gwamnonin suna bin dokokin kare hakkin dan’Adam na kasa da kasa da kuma yarjejeniyoyin da Nijeriya ta rattabawa hannu tare da kungiyoyi masu alaka da Majalisar Dinkin Duniya, ya kara da cewa “hukunce-hukuncen kisa a fili kan irin wadannan masu aikata laifuka na iya jawo fushi da korafe-korafe game da cin zarafin dan’Adam da gwamnati ke yi.”

“Gwamnanmu Fasto ne, kuma Kirista mai kishin addini, wanda yake gudanar da al’amuran Cocinsa, don haka na yi imani a matsayinsa na Kirista, ba zai so ya sanya hannu a kan wata takardar hukuncin kisa don a kashe wani ba saboda ba su taba ganin hakan ba

Amma Clifford Thomas, shugaban kungiyar kare hakkin bil’adama ta Akwa Ibom (AIHRC) ya bayyana cewa aiwatar da hukuncin kisa da aka yanke wa masu laifi, duk da cewa tsarin mulki ya tanada, zai iya zama rashin adalci idan bayan shekaru, aka sani cewa wanda aka kashe ba shi da laifi, kamar yadda yake faruwa a Nijeriya da sauran kasashen da suka ci gaba.”

 

Gwamnatin Abia ba ta da ra’ayin aiwatar da hukuncin kisa

A cewar gwamnan Jihar Abia, Aled Otti, dole ne kowane hukunci ya kasance yana da martani, amma wani lokacin “lamarin ba haka yake ba, wanda kuma yin hakan yana da matukar muhimmanci”.

“Idan za ku iya tunawa a makon da ya gabata, gwamnan, bisa ga karimcinsa, ya tabbatar da sakin wasu mutane uku da suka shafe shekaru 26 a kan hukuncin kisa a Legas. Sakon da ke cikin wannan shi ne, yana son hukumomi su yi tunani sosai kan yadda za a aiwatar da hukuncin kisa na wadanda aka yanke wa hukunci.”

An hana LEADERSHIP Weekend bayani kan adadin fursunonin da aka yanke musu hukuncin kisa a shalkwatar hukumar gyaran hali NCS ta Jihar Abia bisa dalilan tsaro.

Wata majiya mai tushe, wacce ta nemi a sakaya sunanta, ta lura cewa saboda azancinsa, yawanci ana bukatar irin wadannan bayanan kuma ana ba da su ne kawai akan umarnin Kwanturola Janar.

Amma Stan Elekwa, wani mai fafutukar kare hakkin bil’adama, ya ba da shawarar a mayar da irin wannan hukuncin zuwa gidan yari na dogon lokaci, “kamar yadda ya kasance a wasu al’ummomin yanzu.”

 

Wani Lauya a Kaduna ya bayyana dalilin da ya sa ba a zartar da hukuncin kisa ga wadanda aka hukunta

Wani lauya mazaunin Kaduna, Hiifan Abuul, ya shaida wa LEADERSHIP Weekend a Kaduna cewa, “Dokokin hukunta laifukan da ake fayyace laifuka a karkashinsu su ma sun tanadi hukuncin haka.

“Hukuncin kisa a cikin dokokinmu na laifuka hukunci ne na manyan laifuffuka kamar kisan kai” ko da yake yanke hukunci a koyaushe yana hannun alkali mai shari’a. A wasu lokuta, suna iya daukar daurin rai da rai a matsayin hukuncin kisa,” Abuul ya kara da cewa.

 

Rikicin kare hakkokin dan’adam ne ya hana zartar da kisan fursunoni – Mataimakin Gwamna Otu

A Jihar Kuros Riba, Sakataren Hukumar Kula Da Harkokin Shari’a ta Jihar Cross Riber, Barista James Ibor ya bayyana matsalolin da kundin tsarin mulkin kasar ya tanada a matsayin wadanda ke da alhakin aiwatar da hukuncin kisa ga fursunonin da aka yankewa hukuncin kisa a Jihar.

Ibor ya bayyana cewa, shekaru da dama da suka gabata, Gwamnatin Jihar Kuros Riba ta yi biyayya ga manufar kungiyar Amnesty International na hana kisa ga fursunonin da aka yankewa hukunci, yana mai jaddada cewa shi kadai ke hana gwamnatin jihar aiwatar da hukuncin kisa ga fursunoni.

“Alhamdu lillahi, duk gwamnonin Jihar Kuros Riba sun amince da wannan manufar, kuma da yanayin ci gaban kimiyyarmu, gwamnati ta ba da damar gyara kuskure, me zai faru idan wani wanda aka yanke masa hukunci ya zama ba daidai ba?” Ya tambaya.

Ibor ya bayyana cewa bai wa mutanen da aka yankewa hukuncin kisa, hukuncin daurin rai da rai ya fi dacewa da su, saboda, a wasu lokuta, sabbin hujjojin da ke wanke fursunonin na iya fitowa, yana mai jaddada cewa yana da sauki a biya irin wadannan fursunonin diyya.

“Bincike ya nuna cewa hukuncin kisa ba abu ne da za a hana aiwatar da shi ba, sai dai da zarar ka zartar da hukuncin kisa, saboda kawai an yanke wa wanda ake tuhuma, to da wuya a sauya hukuncin a lokacin da wasu sabbin bayanai suka bayyana wadanda ke wanke mutumin daga aikata laifin.”

Kokarin neman babban lauyan gwamnati da kwamishinan shari’a na Cross Riber ya yi magana kan lamarin ya ci tura. Bai amsa sakon tes da kiran waya da aka aika masa ba, kuma bai sake kiran wakilanmu ba.

 

Gwamnonin suna tsoron kashe wadanda ba su ji ba ba su gani ba

Mai ba gwamnan Jihar Cross Riber shawara na musamman Barista Ekpeyong Akiba ya bayyana cewa, kasadar aiwatar da hukuncin kisa ga wadanda ba su ji ba ba su gani ba, na daya daga cikin manyan dalilan da ya sa gwamnatoci suka kasa aiwatar da hukuncin kisa.

Ya jaddada cewa baya ga alakarta da kungiyoyin farar hula da kuma kungiyoyin kasa da kasa da dama, gwamnati na mutunta mutunci da tsarkin rayuwar dan’Adam.

 

Karancin hukuncin rataya

Ya kuma kara da cewa, rashin zartar da hukuncin rataya shi ma wani abu ne na yaki da kashe-kashen da ake yi wa fursunonin da ake yankewa hukuncin kisa a jihar.

“Lokacin da aka yanke wa masu laifi hukuncin kisa, gwamnati kan sha wahala a wasu lokutan saboda rashin rataya da ke tabbatar da cewa wadanda shari’a ta hukunta sun bi ta hanyar da ta dace, ko a Nijeriya ban san ko muna da masu rataya ba.

“Yana da wahala ka ji an yi rataya a wajen kasar. Masu zartar da hukuncin, wadanda muke kira masu rataya, suna da wahalar samuwa,” in ji shi.

Ziyarar da aka kai shalkwatar hukumar da ke Calabar a Jihar Cross Riber a ranar Laraba ba ta dawo da sakamako ba.

Shugaban hukumar na jihar, Mista Richard Moses Williams, ba zai bayyana ainihin adadin fursunonin da aka yanke musu hukuncin kisa ba.

 

Ba’a aiwatar da hukuncin kisa a Katsina

Wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa Jihar Katsina ba ta ci gaba da aiwatar da hukuncin kisa ga fursunonin da aka yanke musu hukuncin kisa ba, duk da cewa akwai mutanen da aka yanke musu hukuncin kisa.

Jami’ai sun ce an dakatar da aiwatar da hukuncin kisa ne saboda wasu dalilai da suka hada da: daukaka kara, da kin sanya hannu kan sammacin kisa da gwamnan ya yi, da kuma karuwar matsin lamba daga masu rajin kare hakkin dan’Adam.

“Dokar ta bai wa gwamnan damar ba da izinin aiwatar da hukuncin kisa, amma hakan ba ya faruwa a ‘yan shekarun nan,” in ji wani babban jami’in gyaran hali. “Yawancin gwamnonin suna taka-tsantsan saboda damuwar gida da waje game da hukuncin kisa.”

Yayin da Hukumar Kula da Gyaran Hali ta Nijeriya (NCS) a Katsina ba ta fitar da ainihin adadin fursunonin da aka yanke wa hukunci ba a shekarar 2025, majiyoyi sun tabbatar da cewa adadin mutanen da ake yanke wa hukuncin kisa na karuwa. Mutane da yawa sun shafe sama da shekaru 10 suna jiran kisa.

Nauyi da tsadar kudin da ake kashewa na karuwa. Yayin da ake kashe Naira 750 na ciyar da kowane dan gidan yari da dubunnan fursunoni a fadin jihar, kasafin kudin abinci na shekara ya kai daruruwan miliyoyin Naira, wanda kaso mafi yawa daga cikin wadanda ke daure da su a gidan yari ne ko kuma wadanda ake hukuntawa ke amfanar su.

Kasafin kudin Katsina na 2025 ya ware kudade don tallafa wa gidajen yari, amma ba a bayyana alkalumman da suka shafi hukuncin kisa ba.

Shugaban kungiyoyin farar hula a Katsina Abdurahaman Abdullahi, ya ce ba kasafai ake bin diddigin hukuncin kisa a bainar jama’a ba.

“Wasu suna faruwa, amma ba a ba da rahotonsu ba, idan ya zamto shari’ar ba ta janyo hankalin mutane ba sai a manta da su” in ji shi.

 

Fursunoni 50 ne a Jihar Jigawa ke jiran kisa

A cewar babban lauyan gwamnatin Jihar Jigawa kuma kwamishinan shari’a Honarabul Bello Abdulkadir Fanini, rahoton karshe da aka samu daga hukumar gidan yari ya nuna cewa adadin fursunonin da ake yankewa hukuncin kisa a jihar sun kai 50.

Ya yi nuni da cewa 38 ne wata babbar kotun jiha ta yanke musu hukunci, yayin da 12 aka sauya shari’arsu zuwa wasu hukunce-hukuncen.

Hon Fanini ya bayyana wasu manyan abubuwa guda uku da ke kawo jinkirin aiwatar da hukuncin: Tsarin shari’a, wanda wasu shari’o’in ke kan kararraki ba a kammala ba, yayin da wasu kuma aka mayar da su gidan yari.

 

“Wani lokaci a matsayinmu na masu ba da shawara kan harkokin shari’a, muna ba gwamna shawara da ya yi musu afuwa gaba daya bayan sun shafe shekaru a gidan yari tare da nuna kyakykyawan dabi’u a gyaran hali,” in ji kwamishinan.

 

Sakin fursunonin da aka yankewa hukuncin kisa bayan shekara 20

Shugaban Kungiyar ‘Cibil Rights Realization and Adbancement Network’ Barista Olu Omatayo ya bayar da shawarar a saki fursunonin da aka yanke musu hukuncin kisa da suka shafe shekaru 20 ko sama da haka.

Ya ce wadanda suka shafe shekara 20 ko sama da haka a kan hukuncin kisa dole ne sun koyi darasinsu kuma za su taimaka wa al’umma da kansu.

“An yi ta neman a soke hukuncin kisa saboda kasashe da dama sun soke shi. Fursunonin da suka shafe shekaru 20 ko fiye da haka ya kamata a ‘yantar da su, yayin da wadanda suka share shekaru 10 ko sama da haka a mayar da su gidan yari,” in ji shi.

Wata majiya a gidan gyaran hali ta Enugu ta shaida wa wakilinmu cewa, farashin ciyar da kowane fursuna a kullum ya kai Naira 1,125, wanda ya karu daga Naira 750 a watan Janairun 2025.

A Enugu dai ba a dade da samun rahoton rattaba hannu kan sammacin kisa ba. Duk da haka, a cikin ikonsa na jin kai, Gwamna Peter Mbah kwanan nan ya saki wasu fursunoni tare da yin afuwa ga wani da aka yi masa afuwa.

Karimcin na da nufin yin amfani da hakkinsa na jinkai don rage cunkoso a cibiyar gyaran hali ta jihar.

 

Kasafin ciyar da fursunoni bai wadatar ba – Kwanturolan Bayelsa

Kwanturolan hukumar gyaran hali ta Nijeriya a Jihar Bayelsa, Imo Ikahokhuele, ya ce alawus-alawus na ciyarwa na Naira 1,125 ga kowane fursuna a kowace rana bai wadatar ba.

Da yake zantawa da LEADERSHIP Weekend game da kalubale da tsadar kayan aikin gidan gyaran hali, ya bayyana cewa a baya gwamnatin tarayya ta ware Naira 750 ga kowane fursuna a kullum amma a baya-bayan nan ta kara shi zuwa Naira 1,125. Yayin da wannan kari ya zama mai fa’ida, hakan ya rage yawan abin da ake bukata don samar da abinci mai kyau, musamman a cikin tashin farashin abinci da hauhawar farashin kayayyaki.

Ya ce, “Ba za ku iya tantance jimillar kasafin kudin kula da fursunoni ba, kula da ababen more rayuwa, kiwon lafiya, tufafi, samar da ruwan sha, da samar da janareta duk sun fada cikin kasafin kudi.

Ya bayyana cewa a halin yanzu Bayelsa na tsare da fursunoni kusan 691, kasa da kusan 700 a makon da ya gabata. Kula da su yana bukatar albarkatu masu mahimmanci, gami da kudi don abinci, ruwa, kiwon lafiya, da wutar lantarki.

Ikahokhuele ya kara da cewa “Idan aka samu barkewar cututtuka, kamar cutar masassharar kaji, kawo dauki ya zama dole domin kare hakkin fursunoni.”

 

Kin sanya hannu akan sammacin kisa, cin amanar adalci ne

Shugaban kungiyar kare hakkin jama’a ta Jihar Bayelsa, Kwamared Dabid West, ya soki gwamnonin jihohin da kin sanya hannu kan sammacin kisa na wadanda aka samu da laifi.

Ya ba da shawarar gwamnoni kan su ji tsoron sakamako na dabi’a ko na addini akan nauyin ba da izinin kisa.

West ya ce, “Gwamnoni suna fargaba, watakila suna tsoron ‘jinin wani mutum’ zai rataya a wuyansu, amma doka ta bukaci sa hannunsu. kin sanya hannu a kan fursunonin da aka yankewa hukuncin daurin rai da rai a cikin kudin jihar yazama rashin adalci. Gwamnonin da suka ki sanya hannu ba su cancanci samun mukami ba.”

 

Ra’ayin shari’a kan sa hannu a takardar hukuncin kisa

Lauya mai kare hakin bil’adama Barista Anthony Ndeze ya bayyana cewa a bisa ka’ida ba a tilasta wa gwamnoni sanya hannu kan sammacin kisa; Yayin da doka ta ba da izinin yanke hukuncin kisa, gwamnoni na iya yin afuwa bisa yanayi ko imani.

Ko’odinetan Kungiyoyin ‘Yancin Jama’a na Arewa ta Tsakiya (CLO), Kwamared Stebe Aluko, ya ce gwamnonin na gujewa sanya hannu kan sammacin kisa saboda dalilai na siyasa, ko fargabar rashin adalci. Yayin da wasu gwamnonin ke yin taka-tsantsan, da yawa ba su da niyyar aiwatar da hukuncin kisa koda kuwa shari’a ta bayyana.

“Gwamnoni na iya yin shakka saboda imani ko tsoron cewa suna da alhakin, amma a gaskiya, sun bi doka, sanya hannu kan takardar ba kisa ba ne – doka ce ta zartar da hukuncin,” in ji shi.

 

Abubuwan siyasa, addini da ke hana aiwatar da hukuncin kisa

Ya kara da cewa al’amuran addini, kabilanci, ko siyasa su kan yi tasiri kan rashin amincewar gwamnonin wajen yanke hukuncin kisa.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

2027: Gangamin ‘Yan Adawa Ya Sa APC Fafutukar Neman Mafita

Next Post

Nijeriya Za Ta Rika Samun Naira Tiriliyan Uku A Aikin Tatsar Rogo Duk Shekara – Kashim

Related

APC
Manyan Labarai

2027: Gangamin ‘Yan Adawa Ya Sa APC Fafutukar Neman Mafita

5 hours ago
Majalisar Dokokin Nijeriya Ta Sanar Da Dakatar Da Ayyukanta Saboda Alhinin Rasuwar Buhari
Labarai

Na Shiga Aikin Soja Domin Gujewa Yin Auren Fari Da Ƙuruciya — Buhari

5 days ago
Ko Yanzu Tinubu Ya Yi Rawar Gani, Kuma Yana Ƙoƙari Sosai – Buhari
Rahotonni

Muhimman Abubuwa 10 Da Kowa Zai So Ya Sani Game Da Marigayi Shugaban Ƙasa Buhari

6 days ago
2027: Shugabannin Hamayya Sun Bazama Neman Goyon Baya A Yankunansu
Manyan Labarai

2027: Shugabannin Hamayya Sun Bazama Neman Goyon Baya A Yankunansu

7 days ago
2027: Masu Ruwa Da Tsaki Sun Bukaci A Kawo Karshen Matsalar Sayen Kuri’a
Rahotonni

2027: Masu Ruwa Da Tsaki Sun Bukaci A Kawo Karshen Matsalar Sayen Kuri’a

1 week ago
jam'iyyu
Rahotonni

Sarkakiyar Da Ke Tattare Da Zaben 2027 Da Yadda Za Ta Kaya

1 month ago
Next Post
Shettima

Nijeriya Za Ta Rika Samun Naira Tiriliyan Uku A Aikin Tatsar Rogo Duk Shekara – Kashim

LABARAI MASU NASABA

sallah

Yadda Hauhawar Farashin Kayan Abinci Ya Ragu A Nijeriya

July 19, 2025
Shettima

Nijeriya Za Ta Rika Samun Naira Tiriliyan Uku A Aikin Tatsar Rogo Duk Shekara – Kashim

July 19, 2025
Fyade

Nijeriya Na Kashe Naira Miliyan 4.3 A Kullum Don Ciyar Da Wadanda Ke Jiran Hukuncin Kisa

July 19, 2025
APC

2027: Gangamin ‘Yan Adawa Ya Sa APC Fafutukar Neman Mafita

July 19, 2025
Dangote

Dalilin Da Ya Sa Dangote Ya Jinjina Wa Hukumar NPA

July 18, 2025
Philippines Na Zama Tushen Tashin Hankali A Tekun Kudancin Kasar Sin

Philippines Na Zama Tushen Tashin Hankali A Tekun Kudancin Kasar Sin

July 18, 2025
2027: Atiku, Obi Da Amaechi Za Su Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Takarar Shugaban Kasa A ADC

2027: Atiku, Obi Da Amaechi Za Su Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Takarar Shugaban Kasa A ADC

July 18, 2025
Kasar Sin Ta Gano Ma’adanin Yuraniyom Mafi Daraja A Karkashin Kasa Mai Zurfi

Kasar Sin Ta Gano Ma’adanin Yuraniyom Mafi Daraja A Karkashin Kasa Mai Zurfi

July 18, 2025
majalisar kasa

Kirkirar Sabbin Jihohi Da Kananan Hukumomi Sun Dabaibaye Sauraron Jin Ra’ayoyin Gyaran Tsarin Mulki

July 18, 2025
Ƙwallon Mata: Nijeriya Ta Lallasa Zambia Da Ci 5-0

Ƙwallon Mata: Nijeriya Ta Lallasa Zambia Da Ci 5-0

July 18, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.