Gwamnatin Tarayya, ta tabbatar da cewa ta kammala biyan bashin dala biliyan 3.4 da ta karɓa daga Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) domin yaƙi da cutar COVID-19.
Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin, bayan taron Majalisar Zartaswa da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
- Sin Ta Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Da Ake Iya Sarrafawa Daga Nesa
- Kaico: Wani Ƙani Ya Kashe Saurayin Yayarsa A Kano
Ya ce: “Za mu iya tabbatar da cewa Nijeriya ta fice daga ƙangin bashin IMF. Wannan yana nufin cewa yanzu babu wani bashi da IMF ke bin ƙasarmu.”
Wannan bashi an karɓo shi ne a shekarar 2020 lokacin da cutar COVID-19 ta addabi duniya, domin tallafa wa Nijeriya wajen kula da kiwon lafiya da kuma farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasa wanda annobar ta durƙusar da shi.
A makon da ya gabata ne IMF ta fitar da rahoton da ke nuna cewa Nijeriya ta kammala biyan bashin.
Amma sai yanzu gwamnatin tarayya ta fitar da sanarwa a hukumance.
Masana tattalin arziƙin sun bayyana cewa kammala biyan wannan bashi wata alama ce ta daidaituwar tsarin kuɗi na ƙasar da kuma yunƙurin rage dogaro da lamuni daga ƙasashen waje.
Wasu sun ce hakan na iya ƙara jawo amincewar ƙasashen duniya da hukumomin ba da lamuni ga Nijeriya, musamman idan aka yi la’akari da ƙoƙarin da gwamnatin Bola Tinubu ke yi na farfaɗo da tattalin arziƙi.
Wani ƙarin bayani daga ma’aikatar kuɗi ya ce an biya bashin ne a matakai daban-daban tun daga shekarar 2021, kuma an kammala biya a farkon shekarar 2025.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp