Bankin Duniya ta mika dala biliyan 1.5 a matsayin rancen waje ga Nijeriya a cikin yunkurin gwamnatin tarayya na aiwatar da cire tallafin man fetur da kuma yin kwaskwarima ga dokar haraji.
Wannan na kunshe ne a bayanin rancen da Bankin Duniyar ya fitar a baya-bayan nan.
Rancen wanda zai taimaka wajen farfado da tattalin arziki da aiwatar da manufofin kyautata harkokin kudi a cikin watanni shida.
- Gwamna Fintiri Ya Nada Sabbin Sarakuna 7 A Jihar Adamawa
- Bayan Cire Tallafin Mai Da Gyaran Dokar Haraji, Bankin Duniya Ya Danƙa Wa Nijeriya Bashi
Bayanin bankin ya nuna cewa an amince da bashin ne a ranar 3 ga watan Yunin 2024, kuma an sake kason farko na dala miliyan 750 a ranar 2 ga watan Yulin 2024, yayin da kuma aka turo wa Nijeriya sauran kudin a watan Disamba.
Kudin na dala biliyan 1.5 an bai wa Nijeriya da tsarin biya a lokuta daban-daban da nufin taimakawa wajen gudanar da ayyukan da za su farfado da tattalin arziki.
Rancen farko na dala miliyan 750 da aka samu daga kungiyar ci gaban kasa da kasa na da tsawon shekaru 12 domin a biya. Yayin da kuma rance na biyun wato na dala miliyan 750 shi kuma za a biya shi a cikin shekaru 24 masu zuwa.
A cewar Bankin Duniyan, rancen da ta bai wa Nijeriya za ta taimaka wajen aiwatar da manufofin da za su kai ga farfadowa daga cire tallafin mai da daidaita musayar canjin kudi da kuma manufofin haraji.
Idan za a tuna dai a watan Oktoban 2024, gwamnatin tarayya ta mika kudirin gyara dokar haraji ga majalisar dokoki na kasa domin neman amincewa, wanda dokar ta janyo cece-kuce a tsakanin ‘yan Nijeriya, musamman shugabannin Arewa da suke zargin dokar ka iya janyo musu nakasu.
“An kuma aiwatar da garambawul don daidaita kasuwar man fetur gabaki daya, tare da tabbatar da cewa an kayyade farashin kayayyaki bisa yanayin kasuwa da bude fannin gasa. Hukumomin suna bin diddigin alkawarin da suka yi na dakatar da kasafin kudi tare da dogaro da daidaitattun kayan bashi don samar da givin.”
A halin da ake ciki, a cikin watannin da suka gabata, tsarin tagwayen manufofin gwamnati na cire da tallafin man fetur da hadewar musayar kudade ya jawo yabo, yayin da wasu kuma suka yi ta yir da su.
Musamman, a karkashin manufofin, farashin man fetur ya karu sau biyar, kuma farashin canji ya karu, wanda ya janyo tsadar rayuwa ga yawancin ‘yan Nijeriya.
Ko da yake gwamnatin tarayya ta vullo da hanyoyin yayyafa ruwa ga matsalar, kamar bayar da naira 25,000 ga gidaje, wanda gidaje miliyan biyu suka amfana, aiwatar da shirin amfani da motoci masu amfani da iskar gas, wanda shi ne mafi arha a kan mai don rage tasirin cire tallafin mai.
Lamarin ya janyo har tasirin hauhawar farashin kayan abinci, ya haura zuwa kashi 34.60 da kashi 39.93, bi da bi.