Tawagar ‘yan wasan Super Eagles ta Nijeriya ta yi kasa zuwa mataki na 42 a jerin wadanda ke kan gaba a kwallon kafa a duniya kamar yadda hukumar kwallon kafa ta FIFA ta sanar.
A jadawalin da FIFA ta fitar ranar Alhamis, Nijeriya ta barar da maki 16.04, wadda ta hada 1474.44, wadda take da maki 1490.48 a cikin Oktoba, sai bi wannan koma bayan bai shafi matakin Super Eagles a nahiyar Afirka ba, har yanzu tana nan a matsayi na shida.
- Manoman Karkara Sun Nuna Farin Ciki Da Yadda Suka Amfana Da Tallafin IFAD
- Kayan Da Nijeriya Ke Fitarwa Waje Sun Karu Zuwa Naira Tiriliyan 10.35
Biyan da Morocco da Senegal da Tunisia da Algeria da kuma Masar ke jerin wadanda ke kan gaba a iya kwallo a Afirka kuma wannan makin da Nijeriya ta barar ya biyo bayan tashi 1-1 da Lesotho da kuma Zimbabwe shima 1-1 a wasannin neman shiga gasar kofin duniya.
A fadin duniya kuma baki daya har yanzu Argentina ce ta daya a duniya, sai Faransa ta biyu da kuma Ingila ta uku a sahun farko-farko, yayin da Belgium ta yi sama zuwa mataki na hudu.
Brazil ta ci karo da koma baya, wadda ta koma ta biyar ta rasa gurbi biyu, hakan ya biyo bayan doke ta da Colombia da Argentina suka yi a wasannin shiga gasar kofin duniya a yankin Kudancin Amurka.