Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ƙara tabbatar wa da gwamnatin Amurka cewa Nijeriya na kan turbarta na tabbatar da ‘yancin ‘yan jarida da kafafen yaɗa labarai.
Ya ce, akwai buƙatar wannan ‘yanci sosai domin ta hanyar kafafen yaɗa labarai ne dimokuraɗiyya ke ƙara karsashi, tasiri da nagarta a cikin zukatan al’umma.
- Minista Ya Biya Tarar Naira Miliyan 585 Domin A Saki Daurarru 4,068
- Manufar Sin Ta Baiwa Kasashe Damar Shigowa Kasarta Ba Tare Da Biza Ba Za Ta Bunkasa Mu’amala Tsakanin Jama’a Da Jama’a
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar da mataimaki na musamman a fannin yaɗa labarai ga ministan, Malam Rabi’u Ibrahim, ya fitar a ƙarshen mako.
Ministan ya bayyana haka a lokacin da Babban Jami’in Amurka mai Kula da Al’amurran Nijeriya, Mista David Greene, ya kai masa ziyara a ofishinsa.
Ya ce: “A yayin da mu ke goyon baya da tabbatar da ‘yancin kafafen yaɗa labarai da na ‘yan jarida, mu na kuma yin kira ga gwamnatin Amurka da ta ba mu goyon baya ta hanyar ƙara zurfafa horaswa ga ‘yan jarida, musamman a fannin binciken tabbatar da gaskiya da fayyace sahihin labari daga labaran bogi.”
Idris ya ƙara da cewa, “Yin hakan zai ƙara rage yawan watsa labaran bogi, bayanan karkatar da hankalin jama’a, da rage bazuwar ji-ta-ji-ta acikin al’umma.”
Ministan ya jaddada aniyar da Nijeriya ta sa a gaba wajen ƙara wa dimokuraɗiyya daraja da ƙima, ya na mai cewa, “Muhimmin abu ne a matsayin Amurka na babbar ƙawar Nijeriya ta ƙara zurfafa goyon bayanta ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, a ƙoƙarin da gwamnatin ke yi na bunƙasa tattalin arzikin ƙasar.”
A jawabin sa, Mista Greene ya ce Amurka na goyon bayan Nijeriya ɗari bisa ɗari wajen inganta dimokuraɗiyya da inganta ayyukan kafafen yaɗa labarai.
Ya ce an keto shekaru da dama ƙasarsa ta na bayar da guraben ƙaro ilmi, bada horaswa da kuma fannin inganta tsaro.