Nijeriya ta kammala gasar wasannin nakasassu ta shekarar 2024 a birnin Paris da samun lambobin yabo bakwai da suka hada da zinare biyu, da azurfa uku, da tagulla biyu, inda ta zo ta 40 cikin kasashe 83.
‘Yar wasan Nijeriya mai suna Folashade Oluwafemiayo ce, ta jagoranci nasarorin, inda ta samu lambar zinare tare da karya tarihin duniya guda biyu a bangaren mata masu daga nauyin kilo 86.
- Babu Bukatar Tada Hankali Kan Karuwar Farashin Mai – IPMAN Ga ‘Yan Nijeriya
- “Babu Gaskiya A Takardar Da Ke Alaƙanta Gwamnatin Zamfara Da ’Yan Bindiga”
Ta zama ‘yar wasa ta farko da ta samu wannan nasara, inda ta tabbatar da matsayinta na zakarar Paralympic sau biyu.
Ita ma Onyinyechi Mark ta dauki zinari a Para-powerlifting, yayin da Flora Ugwunwa, Esther Nworgu, da Bose Omolayo, wadanda suka samu azurfa a bangaren Para-powerlifting mai nauyin kilogiram 79, sun bayar da gudunmawar lambobin yabo da bajintar da suka nuna.
Eniola Bolaji ta kafa tarihi bayan ta samu kyautar tagulla a wasan badminton.
An kammala wasannin ne a filin wasa na Stade de France, inda kasar Sin ke kan gaba a teburin gasar bayan da ta karya tarihin duniya da kyaututtuka 29.