Saurayin da ya banka wa ‘yar wasan Olympics ta kasar Uganda, Rebecca Cheptegei wuta shi ma ya mutu, bayan kunar da ya samu a lokacin da ya ke kunna wutar.
Tsohon saurayin mai suna Dickson Ndiema ya zuba mata fetur ne, ya kona ta bayan da ta koma gida daga coci a makon da ya gabata.
- Gwamna Uba Sani Zai Kaddamar Da Kwalejin Koyon Aikin Jinya Da Ungozoma A PambeguaÂ
- Tallafi: Tinubu Ya Nuna Son Rai Wajen Raba Kayan Abinci – Kwankwaso
Rahotanni sun ce ‘yar wasan da tsohon saurayin nata sun kasance suna rikici kan wani karamin fili da ke arewa maso yammacin Kenya, inda marigayiyar ta ke zaune.
Talla
Ndiema ya mutu ne a daren ranar Litinin a sashen kula da lafiya da ke Moi Teaching and Referral Hospital, inda aka kwantar da shi domin jinya.
Talla