Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana takaicinsa na watsi da ka yi da fannin kiwon dabbobi a Nijeriya, wanda hakan ya yi sanadiyyar karancin samar da Madarar Shanu da ake fitarwa zuwa kasashen waje tare da tafka asarar kudin shiga har kimanin dala biliyan 1.5.
Kazalika, shugaban ya yi nuni da cewa, “Lokaci ya yi da ya kamata mu yi abin da ya dace, musamman idan aka yi la’akari da cewa; wannan kasa na dauke da al’umma sama da miliyan 200, don haka bai kamata a gaza shayar da ‘ya’yanmu Madara ba; a lokacin da suke daukar darussa a Ajujuwansu na karatu a kullum ba”.
- Dalilan Masu Kiwon Kajin Gidan Gona Na Rungumar Sabuwar Dabarar Kiwo A Kano
- Yadda Masu Kiwon ‘Yan Tsakin Gidan Gona Ke Ganin Tasku A Kano
Ya bayyana hakan ne, a kwanakin baya lokacin da ya kaddamar da bunkasa shirin farfado da kiwon dabbobi na kasa.
Idan za a iya tunawa, shirin na bunkasa kiwon dabbobin; Shugaba Tinubu ne ya kirkiro da shi, inda kuma ya kafa kwamitin samar da sabon sauyi a fannin a ranar 19 ga watan Yulin 2024, kafin ya kirkiro da masana’antar da za ta sanya ido ga fannin na kiwon dabbobin.
Ya kara da cewa, “Fannin kiwon, abu ne da ke da matukar muhimmanci, kuma za mu ba shi dukkanin kulawar da ta dace, musamman domin dawo da kimar wannan kasa tamu.”
Da yake yin karin haske a kan muhimmancin da fannin ke da shi a wannan kasa, shugaban ya sanar da cewa; ana bukatar litar Madara akalla tan biliyan 0.7.
Ya ci gaba da cewa, ana kuma bukatar tan biliyan 1.48 na Nama da Kwai; shi ma kimanin tan miliyan 1.48, inda ya sanar da cewa; sai dai abin takaicin shi ne, ba a iya samar da wadannan adadi.
Shugaban ya kara da cewa, yawan litar da ake amfani da ita na Madarar, ta kai kimanin 8.7; wacce ta yi daidai da kilo 9 na Nama, sai kuma kilo 3.5 na Kwai da ya kai kimanin kilo 45.
Har ila yau, ya bayar da tabbacin cewa; Nijeriya za ta iya cimma burin da ta sanya a gaba na sake farfado da fannin kiwon dabbobin, duba da cewa fannin na kara habaka tattalin arzikin wannan kasa tare kuma da samar da ayyukan yi ga ‘yan Nijeriya.
Ya kuma sanar da cewa, akwai damammaki da dama da muke iya gani da idanuwanmu, inda ya sanar da cewa; za mu tabbatar da ganin mun samar da kyakkyawan yanayi, musamman domin kasuwancin fannin ya tumbatsa a Nijeriya.