Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya nuna alhini kan rasuwar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, yana mai cewa Nijeriya ta yi babban rashi na ɗan ƙasa mai gaskiya.
Farfesa Osinbajo ya kasance tsohon mataimakin shugaban ƙasa daga shekarar 2015 zuwa 2023 a ƙarƙashin shugabancin Buhari.
- Kakakin Majalisar Wakilai, Abbas, Ya Yi Jimamin Raasuwar Buhari, Ya Ce Mutuwa Ce Da Ta Girgiza Shi
- Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau Jibril Ya Yi Alhinin Rasuwar Buhari
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook a daren ranar Lahadi 13, ga Yulin 2025, Osinbajo ya bayyana cewa ya tattauna da mai dakin Buhari, Aisha Buhari da ɗansa Yusuf, domin isar da ta’aziyyarsa.
Osinbajo ya rubuta cewa: “Ni da matata Dolapo mun samu labarin rasuwar mai girma tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, GCFR, cikin kaɗuwa da alhini.
“Bayan jin labarin, mun kira Hajiya Aisha Buhari da ɗansu Yusuf domin miƙa ta’aziyya da nuna alhini tare da su, iyalinsa da muka yi aiki da su tsawon shekara takwas a ƙasarmu.
“Nijeriya ta rasa ɗan ƙasa na gaskiya, mutum mai cike da sadaukarwa ga ƙasarsa. Tarihi na Shugaba Buhari zai ci gaba da kasancewa abin tunawa cikin ƙima da daraja a aikin gwamnati, Buhari ya dogara da gaskiya da tsari da sadaukarwa ga muradun jama’a.
“Muna roƙon Allah Madaukakin Sarki da ya bai wa iyalansa ƙarfin halin juriyar rashi da kwanciyar hankali, da kuma dukkan masu iyalai Allah ya jikansa, ya kula da bayansa.” cewar Osibanjo
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp