Nijeriya ta fito a matsayin ƙasar da ke da mafi ƙanƙantar tsammanin tsawon rayuwa a duniya, bisa sabon bayanan ƙididdiga ta duniya (Global Statistics) ta fitar.
Rahoton ya nuna cewa Nijeriya ce ta farko a jerin ƙasashen da ke da ƙarancin tsammanin tsawon rayuwa, tana biye da ƙasar Chadi da Sudan ta Kudu, ƙasashen da suka shiga matsayi na biyu da na uku.
- Kamfanin Kasar Sin Ya Bayar Da Gudunmuwar Kayayyaki Ga Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Sudan Ta Kudu
- Rashin Aikin Yi: A Halin Yanzu Masu Digiri Na Sayar Da Fiya Wata Da Aikin Achaba
Haka kuma, Nijeriya ta tsaya a matsayi na 161 daga cikin ƙasashe 175 a jerin ƙasashen da mata ke cikin aminci, abin da ke nuna cewa ƙasar na daga cikin wuraren da suka fi wahalar rayuwa ga mata a duniya.
Denmark, da Switzerland, da Sweden sun kasance a matakai na farko, na biyu da na uku, a cewar bayanan shekarar 2025 da aka wallafa a shafin X na hukumar kididdigar.
A wani ɓangaren, da ke nuni da cewa Jihar Legas ta zama ta farko cikin birane 40 da suka fi muni wajen samun ingantaccen rayuwa a duniya. Rahoton ya nuna cewa yanayin rayuwa a Legas ya fi muni fiye da Tehran (Iran) da Manila (Philippines), da suka biyo baya.
A jerin ƙarshe, birnin Quito na ƙasar Ecuador ya kasance na 40 cikin biranen da ke da mafi ƙarancin ingancin rayuwa, yayin da Delhi (Indiya) da Saint Petersburg (Rasha) suka kasance a matakai na 39 da 3
8 bi da bi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp