Kwastomomin da suke shan wutar lantarki a kasashen Nijar da Togo da Benin sun ki biya bashin sama da Naira biliyan 132.2 na wutar da suka sha.
Aminiya ta rawaito cewa, ana bin su bashin ne sakamakon wutar da suka sha ta tsawon shekara hudu, daga farkon 2018 zuwa watannin uku na farkon 2023.
- Shugaban Nijeriya Ya Aza Harsashin Ginin Sabuwar Tashar Wutar Lantarki Da Kamfanin Sin Zai Gudanar
- Zanga-Zanga Ta Barke A Gaza Saboda Karancin Wutar Lantarki
Wasu alkaluma da rahoton Hukumar Kula Lantarki ta Kasa (NERC) ta fitar sun nuna kasashen sun sha wutar Naira biliyan 180.8 a tsawon lokacin, amma Naira biliyan 48.57 kawai suka iya biya.
A cewar rahoton, Jamhuriyar Benin ce dai a kan gaba wajen taurin bashin da Naira biliyan 72.1, ta hannun kamfanin lantarkin kasar mai suna SBEE, sannan sai Jamhuriyar Nijar mai Naira biliyan 31.3 ta kamfaninsu mai suna NIGELEC.
Ita kuwa kasar Togo a cewar rahoton na NERC, ana bin ta bashin Naira biliyan 10.3 ta hannun kamfanin lantarkinta mai suna CEET.
Kazalika, rahoton ya nuna a shekara ta 2018, ƙasashen sun biya Naira miliyan 650 daga bashin biliyan 47.25 da ake bin su, yayin da a 2019 suka ki biyan ko sisi daga bashin biliyan 40.6.