Shugaba Bola Tinubu ya yi alƙawarin hanzarta aiwatar da ci gaban Nijeriya ta hanyar amfani da fasahar kere-kere da tattalin abinci don samun nasarori irin na sauran ƙasashe masu tasowa kamar Brazil.
A yayin da yake jawabi a ranar Talata a lokacin da ya gana da wasu ‘yan Nijeriya mazauna kasar Brazil, shugaba Tinubu ya jaddada kudirin gwamnatinsa na kawo sauyi ta hanyar kere-kere, gyare-gyare, da kuma samar da ci gaba mai dorewa.
- Sin Da Kasashen Afirka Za Su Rubuta Sabon Babin Hakkin Dan Adam Bisa Ci Gabansu
- NRC Ta Dakatar Da Sufurin Jirgin Ƙasan Abuja-Kaduna Bayan Hatsarin Da Ya Yi
“Dole ne mu sanya Nijeriya a gaba wajen ci gaban Afirka, ta hanyar amfani da fasahar kere-kere, tattalin abinci, da jajircewa wajen sauya irin kaddararmu,” in ji Tinubu a wata sanarwa da kakakinsa, Bayo Onanuga ya fitar.
A cewar Tinubu, Nijeriya da Brazil a wani lokaci sun taba zama a matsayi daya. “Amma duba Brazil a yau, fasaharta da tsarin tattlin abincinta. Dole ne mu tambayi kanmu: menene suke da shi wanda ba mu da shi? Muna da ilimi, makamashi, da matasa. Muna da duk abin da muke bukata. Yanzu, dole ne mu tashi tsaye mu yi aiki.”
Da yake yabawa al’ummar Nijeriya mazauna kasashen waje, Tinubu ya bukace su da su dauki kansu a matsayin masu ruwa da tsaki wajen gina sabuwar Nijeriya mai tushe a fannin fasahar kirkire-kirkire, al’adu, da kuma aiki tare.
Ya amince da matsalolin da ‘yan kasar ke fuskanta sakamakon sauye-sauyen tattalin arziki da ake ci gaba da yi, yana mai jaddada cewa wadannan muhimman matakai ne na tabbatar da ci gaban kasa da za a gani nan gaba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp