Hukumar kula da yanayi ta Nijeriya, NiMet, ta yi hasashen samun hadari, tsawa da kuma mamakon ruwan sama daga ranar Litinin zuwa Laraba a fadin kasar nan.
Hasashen yanayin na NiMet da aka fitar a ranar Lahadi a Abuja, ya yi hasashen sararin samaniya a ranar Litinin da tazarar hasken rana a yankin Arewa da safiya.
- Kwankwaso Ba Zai Yi Wa Peter Obi Takarar Mataimaki Ba — NNPP
- Farashin Gas Din Girki Ya Kara Yin Tashin Gwauron Zabi — NBS
A cewarta, ana sa ran samun tsawa a sassan jihohin Taraba, Bauchi, Borno, Yobe, Adamawa, Gombe, Kaduna, Kano, Jigawa, Katsina, Zamfara da Sakkwato a cikin sa’o’i da rana.
Hukumar ta yi hasashen yanayi na gajimare a yankin Arewa ta tsakiya da safe.
An yi hasashen za a yi tsawa a wasu sassan Kogi, Kwara, Filato, Benue, Neja da kuma babban birnin tarayya Abuja.
NiMet ta yi hasashen yiwuwar samun ruwan sama a jihohin Cross River, Rivers da Bayelsa.
Ta kuma yi hasashen samun tsawa a jihohin Enugu, Ondo, Edo, Imo da Anambra da yammacin ranar Litinin tare da yiwuwar samun ruwan sama a jihohin Akwa Ibom, Delta, Cross River, Rivers da Bayelsa.
“A ranar Talata ana sa ran za a yi tsawa a sassan jihohin Borno, Adamawa, Taraba, Bauchi, Jigawa, Yobe, Gombe da Kaduna. Ana sa ran iska mai karfi za ta ke kadawa tare da tsawa musamman jihohin Borno da Yobe da kuma Jigawa.
“A washegari, ana sa ran za a yi tsawa a sassan jihohin Kano, Katsina, Kaduna, Zamfara, Kebbi da Sakkwato.
Hukumar ta yi hasashen yiwuwar samun tsawa a wasu sassan Filato, Kogi, Nasarawa, Neja da kuma babban birnin tarayya.
An yi hasashen za a samu ruwan sama a jihohin Enugu, Ogun, Ondo, Edo, Bayelsa, Rivers, Cross River da kuma Legas da rana da yamma.
“A ranar Laraba, ana sa ran za a yi tsawa a sassan jihohin Taraba, Bauchi, Borno, Gombe, Kaduna, Kano, Jigawa, Katsina, Zamfara da Sakkwato da safe.
“A washegari, akwai yiwuwar tsawa a wasu sassan jihohin Yobe da Adamawa.
“Ana sa ran samun hadari a yankin da yiwuwar yin tsawa a sassan Nasarawa, Kwara da kuma Babban Birnin Tarayya da safe.
“An shawarci ma’aikatan jirgin sama da su samu sabbin rahotannin yanayi daga NiMet don inganta yanayin ayyukansu,” in ji shi.