Mataimakin Kwanturola Janar na Hukumar Shige da Fice ta Kasa (NIS), ACG James Sunday, ya ziyarci kwamandan rundunar Operation Hadin Kai a hedikwatar hukumar da ke Arewa maso Gabas a Maiduguri a karkashin jagorancin Manjo Janar W Shaibu domin tattauna gudunmawar da hukumar za ta bai wa rundunar a Maiduguri.
Taron ya samu halartar Babban Kwanturolan hukumar reshen Jihar Borno, CIS Abba Salihu da mataimakansa da ke shiyyar C, Manjo Janar W Shaibu da sauran manyan hafsoshin soji da ke hadin gwiwa da rundunar.
- Kannywood Wuri Ne Na Nishadi Ba Gyaran Tarbiyya Ba -Fauziyya D Suleiman
- Abubuwan Da Za Su Taimaka Wa Mai Azumi Ya Kasance Cikin Koshin Lafiya
Ko’odinetan Shiyyar C (Arewa maso Gabas), wadda ta kunshi jihohin Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Yobe da Filato bayan sun ziyarci jihar Yobe, ya ziyarce su ne domin tantance ayyukan rundunar tare da jadadda umarnin sake bude iyakar Nijeriya da Jamhuriyar Nijar, sannan zai dawo Maiduguri domin ci gaba da ziyarar aikin kwanaki biyu a jihohin Borno da Yobe.
Haka zalika hukumar ta umarci rundundar da ke Jihar Borno da ta sake bude iyakar Nijeriya ci gaba da zirga-zirgar mutane zuwa Nijeriya da da sauran al’amuran yau da kullum kamar da yadda aka saba a baya.
Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa tana da jami’ai da maza kusan 230 da aka tura zuwa rundunar hadin gwiwa, domin kyautata dangantakar ta aiki da hadin kai.
A cewar Kwamandan, jami’an NIS sun kware sosai wajen aikinsu dangane da shige da fice da sauransu. Jami’an sun samu horo da tsarin aiki karkashin jagorancin Manjo Janar W Shaibu kamar yadda aka bayyana a yayin taron.
“Ni da kaina na taso daga Maiduguri zuwa Damaturu domin tantance yanayin aikin da ake yi”, in ji ACG James.
“Ina tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa an samu kwanciyar hankali da tsaro a yankin Arewa maso Gabas, harkokin tattalin arziki da na cikin gida sun dawo a jihohin Barno da Yobe, motoci suna zirga-zirga cikin lafiya tare da kayayyaki zuwa sassan kasar nan.
“Ina mika godiya ga dukkan jami’an da ke kan hanyar da sojoji ke aiki ba dare ba rana a kewayen tafkin Chadi da kan iyaka, wannan namijin kokari ne kuma abun a yaba ne, in ji shi.
“Ina son jinjina wa jami’ain NIS tare da mika godiyata a gare su.”
Gwamnatin Jihar Borno ta za ta shirya wani babban taron tsaro a Maiduguri, bisa tsarin NIS a yankin Arewa Maso Gabas, don samar da hanyoyin da za a tabbatar da tsaro da zaman lafiya a yankin a kamar yadda mataimakin gwamnan jihar, Umar Usman Kadafur ya bayyana a lokacin da ya ziyarci ofishin hukumar na shiyyar C, da ke gidan gwamnatin jihar a Maiduguri.